Da Duminsa: A karon farko, Shekarau ya fita rangadi da sabon shugaban APC na tsaginsu a Kano

Da Duminsa: A karon farko, Shekarau ya fita rangadi da sabon shugaban APC na tsaginsu a Kano

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya hallarci taro da sabon shugaban APC na tsaginsa, Ahmadu Haruna Zago
  • Sun hallarci taro ne na musamman da Shekarau ya shirya don tallafawa mutanen mazabansa a Kano ta tsakiya
  • Ganin Shekarau tare da Zago tare a wurin taron ya karfafa jita-jitan da ake yadawa na cewa shi ya yi ruwa da tsaki Zago ya ci zabe

Kano - An gano tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, a ranar Talata, a wurin taro tare da Ahmadu Haruna Zago, shugaban jam'iyyar APC na tsagi guda a jihar Kano

An gan su ne a wurin taron bawa al'umma tallafi da Shekarau, Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya ya shirya kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

Read also

Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa

Da Duminsa: A karon farko, Shekarau ya fita rangadi da sabon shugaban APC na tsaginsu a Kano
Sanata Ibrahim Shekarua da Ahmadu Haruna Zago. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Shirin tsarin tallafi ne na koyar da saka da bada kananan jari ga masu sana'o'i kan ilimin tsafta da amfaninsa a Kano Central da kewaye.

Hukumar yi wa ma'aikatan kula da muhalli ta Nigeria rajista, (EHORECON) da Shekarau ne suka shirya taron.

Hakan ya tabbatar da rahotannin cewa Shekarau yana goyon bayan shugabancin Zago wanda ya zama shugaba a zaben da wani tsagi na APC ta yi.

Abdullahi Abbas tare da goyon baya daga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi nasara a zaben da aka yi wurin taron gangamin APC da aka yi a dakin wasanni na Sani Abacha.

2023: Sai mun tabbatar Tinubu ya zama shugaban ƙasan Najeriya, Adewale

A wani labarin daban, masu fada a ji na jam’iyya mai mulki, APC na reshen jihar Legas sun lashi takobin ganin Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Read also

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

A wata tattaunawa da Vanguard ta yi da sakataren jam’iyyar na jihar Legas, Comrade Ayodele Adewale ya tabbatar da cewa shugabannin APC karkashin Cornelius Ojelabi za su tabbatar Tinubu ya zama shugaban kasa.

Tsohon shugaban karamar hukumar Odofin, Adewale ya yi godiya ga shugabannin jam’iyya akan yin amanna da shi inda ya ce: “Na jajirce wurin yin aiki tare da Hon. Cornelius Ojelabi a matsayin sa na shugaban APC a jihar Legas.

Source: Legit.ng

Online view pixel