Auran matar aure, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Auran matar aure, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan lalata dake faruwa tsakanin matasa na auren matar aure.

Ta iya yiyuwa wani ya yi tambaya cewa ta yaya mutum zai auri matar aure?

Haka tana faruwa ta hanyoyi da dama,

Masali :

1. Mutum ya saki matar sa kafin ta gama idda sai wani ya aure ta, wannan aure bashi da inganci har abada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Mutum ya saki matar sa saki na ɗaya ko na biyu sai ya ce ya mayar da ita, ma'ana ya yi komai, amma sai taƙi ta koma har ta yi idda a haka,( alhalin idan ya mayar da ita idda ta ƙare yanzu ta zama matarsa.)

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Sheƙau: Ya jefa ni cikin ƙunci, ni da shi Shari'a sai a lahira

3. A yiwa wani barazana da kisa ko dauri ko lahanantarwa, idan bai saki matarsa ba sai yaji tsoro ya sake ta ba bisa yardar sa da zaɓinsa da Amincewar sa ba.

4. Ko wani ya saki matar wani, ba da izininsa ba, kuma wani yazo ya aure ta a haka.

Duk waɗannan da makamantan su matan aure ne.

Auran matar aure, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano
Auran matar aure, tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano
Asali: Facebook

Wannan ya sa duk mutumin da zai auri bazawara to ya binciki hanyar da suka rabu da mijinta. Da kuma yadda take yin idda domin ya tabbatar rabuwar a kan shri’a aka yi ta.

Sannan kuma ya tabbatar ta yi cikakkiyar idda. Domin wata matar itama kanta ba ta san hukuncin iddar ba. Wata ta dauka ko da ba ta yi jini ba idan ta yi watanni uku to iddarta ta ƙare.

To akwai wacce sai watanni uku-ukun take yin wata sai shekara shekara take jini wata ma idan ta haihu aka sake ta ba ta fara ganin jini sai bayan ta gama shayarwa sannan ta ga jini, wata kuma sai wata uku uku ta ke ganin jini ka ga irin wannan sai ta yi watanni tara kenan za ta gama idda.

Kara karanta wannan

Kamen Obi Cubana: 'Dan DG na DSS ya caccaki EFCC, ya ce "karnukan 'yan siyasa" ne

Amma mai yiyuwa in ta yi watanni uku ta gaya maka ta gama idda, alhalin jini ɗaya ne ya zo a wata ukun, akwai ragowar watanni biyu..Sai ka aure ta; daga baya sai ka ga cewa ba ta ma fita daga auren wancan mijinta na baya ba balle kai ya halatta ka aure ta. Don haka malamai suka ce anan mace ta yi aure akan aure. Ta yi aure sau biyu.

Don haka dole mutum ya tabbatar cewa bazawarar da zai aura aurenta ya mutu. Sannan kuma ya tabbatar cewa ta yi idda yadda shari’a ta tsara.

A rinka bincike yadda aka rabu da mijin baya da kuma yadda aka yi idda, domin kaucewa yin aure akan aure.

Allah ya ƙara mana sani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel