Da dumi-duminsa: FG ta ce an hada layukan waya miliyan 180 da NIN
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ‘yan Najeriya sama da miliyan 10 sun yi nasarar hada layukan wayar su da NIN a yanzu haka
- A cewar Farfesa Umar Danbatta, mataimakin shugaban hukumar NCC, sama da 'yan Najeriya miliyan 60 ne NIMC ta yiwa rijista
- Shugaban ya bayyana haka ne kwanan nan a Abuja yayin da yake magana a hedikwatar hukumar
A cikin abin da zai ba mutane da yawa mamaki a kasar, idan aka yi la'akari da girmanta, mataimakin shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) Farfesa Umar Danbatta, ya bayyana adadin layukan wayar tarho da aka hada da Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN) a yanzu.
A cewarsa, sama da layukan waya miliyan 180 aka hada a yanzu. Ya bayyana hakan a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa ya fadi wannan ne biyo bayan yiwa 'yan Najeriya sama da miliyan 60 rijista da Hukumar samar da lambar dan Kasa (NIMC) ta yi a cikin bayanan NIN.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da jawabinsa yayin zantawa da Jama'a kan Ka'idoji guda uku kan Tsarin Kare Dokoki a hedikwatar Hukumar a Abuja.
Yan Najeriya Sama da Miliyan 60 Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC
A baya mun kawo cewa hukumar samar da lambar ɗan kasa, NIMC, ranar Alhamis, ta sanar da cewa yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar lambar NIN, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Punch ta ruwaito cewa ya zuwa yanzun NIMC na da bayanan wannan adadin na yan Najeriya a ƙunshin ajiye bayananta (NIDB).
Hukumar ta kara da cewa an samu wannan nasarar ne da haɗin kan masu ruwa da tsaki a ɓangaren, wanda ya haɗa da gaba ɗaya yan Najeriya.
Asali: Legit.ng