Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa

Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa

  • Malam Tulu matukin keke ne da ya tsinci kudin wasu 'yan kasuwa har N500,000 da suka manta da su a kekensa
  • Ya dauka 'yan kasuwan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Yanshanu da ke Jos, amma suka bar jakar kudin
  • Ba tare da bata lokaci ba ya juya kekensa zuwa inda ya sauke su kuma ya tarar da su cike da dimuwa da tashin hankali

Jos - Wani matukin Keke ta haya mai suna Mallam Tulu, ya mayar da kudi har N500,000 zuwa ga wasu 'yan kasuwa bayan sun manta da shi a abun hawansa a Jos, jihar Filato.

Kamar yadda wani Bello Lukman na Unity FM Jos ya wallafa a shafinsa na Facebook, 'yan kasuwan su na kan hanyarsu ta zuwa siyan shanu a yankin Yanshanu da ke Jos a ranar Asabar, 16 Oktoba yayin da suka manta da kudin.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

"Allah ya albarkaci Mallam Tulu, matukin Keke wanda ya dawo wa da fasinjojin 'yan kasuwa kudi har dubu dari biyar da suka manta da su a Kekensa a Jos," ya ce.

Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa
Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa. Hoto daga Bello Lukman Unity FM
Asali: Facebook

Kamar yadda ya wallafa:

"Ya dauka 'yan kasuwan a kan hanyarsu ta zuwa Dengi siyan shanu daga Corona a yankin Yanshanu a Jos. Bayan sun hau Keken a Dilimi, sun samu abun hawa a Dengi sai suka sauka inda suka bar jakar kudinsu a keken.
"Wata budurwa da ta hau keken ta janyo hankalinsa zuwa ga jakar kuma bayan dubawa sai ya ga makuden kudi a ciki. Kai tsaye ya koma inda ya dauka fasinjoji kuma ya tarar da su cike da tashin hankali tare da fatan su samu kudinsu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

"Ya ba su jakar kudinsu kuma sun ba shi har dubu biyar ta nuna godiya da tukuici. Har yau muna da ragowar mazan jiya a kasar nan. Allah ya yi wa Mallam Tulu albarka."

Jerin sunayen jihohin Najeriya 12 da UK ta shawarci 'yan kasar ta da su kiyaya

A wani labari na daban, Ingila ta ce 'yan Boko Haram sun fi son sace wadanda ba 'yan kasar nan ba inda suka ja kunnen 'yan kasar su da tafiye-tafiye zuwa jihohi 12 na Najeriya.

Kamar yadda ofishin FCDO na Ingila ya sanar a ranar Juma'a, Ingila ta ja kunnen 'yan kasar ta tare da basu shawara kan inda ya dace su je, TheCable ta ruwaito.

Gwamnatin Ingila ta ce akwai akwai babbar barazanar cewa ana iya sace mutane a fadin Najeriya saboda a karba kudin fansa ko kuma saboda siyasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel