An yi da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi

An yi da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi

  • An bizne matar marigayi Sheikh Abubakar Gumi da ta rasu ranar Asabar
  • Manyan Malamai da jagororin siyasa sun samu damar halartan jana'izar
  • Ta rasu ta bar 'yaya takwas cikinsu akwai Birgediya Janar AbdulKadir

Kaduna - An gabatar da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu Muhammad Bello matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi.

An yi jana'izar ne bayan Sallar La'asar a gidan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake No 1 Modibbo Adama Road, Unguwar Sarki Kaduna.

Hadimin Dr Ahmad Gumi, Salisu Hassan Webmaster, ya bayyana cewa Dr. Hamza Abubakar Mahmud Gumi wanda dayane daga cikin yayan da ta haifa shine ya jagoranci mata sallah.

A cewarsa, cikin wadanda suka halarci Janazar akwaiDr. Sulaiman Adam Limamin Sultan Bello, Sheikh Balele Wali, Alkali Tahir Lawal Abubakar, Malam Murtala Shanono, Mal Nuhu Alhafiz, Mal Isah Abdullahi Adarkake, Malam Bello Sarkin Malam da Limamin Masallacin Danja Zaria da sauran su.

Kara karanta wannan

Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa

Daga cikin manyan kasa da suka halarta sun hada Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai, mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, da Sanata Musa Bello.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi
An yi da Jana'izar Hajiya Aminatu Bintu matar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gummi Hoto: Sani Webmaster
Asali: Facebook

'Yayan da ta bari

Ta rasu tana da shekaru 86 ta bar 'ya'ya guda takwas maza hudu mata hudu wanda suka hada da:-

Dr. Hamza Abubakar Gumi

Brig. Gen. Abdulkadir Abubakar Gumi

Malam Hassan Abubakar Gumi

Malam Yusuf Abubakar Gumi

Hajiya Ummulkhair Abubakar Gumi

Hajiya Aisha Abubakar Gumi

Hajiya Hauwa Abubakar Gumi

Hajiya Baraka Abubakar Gumi

Hajiya Amina wacce mahaifiya ce ga Brig. Gen. Abdulkadir Abubakar Gumi ta rasu bayan ta yi jinya na 'yan kwanaki a Asibitin Sojoji na 44 dake garin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel