Dan TikTok Ya Sheka Lahira da Damusa Ta Kwamushe Shi ana Bidiyo

Dan TikTok Ya Sheka Lahira da Damusa Ta Kwamushe Shi ana Bidiyo

  • Wata damisa ya hallaka matashi mai shekaru 19 a lokacin da ake daukar bidiyon TikTok a wani wurin kiwon namun daji a Pakistan
  • Rundunar ’yan sanda ta kama mai gonar kiwon namun dajin da kuma wani mai kirkirar bidiyo a kafafen sada zumunta kan lamarin
  • Rahotanni sun ce an saki damisar daga kejin da aka killace ta ne domin daukar bidiyon, amma ta afka wa matashin har ta yi sanadin mutuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wata damisa ta far wa wani matashi mai suna Talha, mai shekaru 19, har ya hallaka shi yayin daukar bidiyon TikTok a wani gidan kiwon namun daji da ke birnin Lahore na kasar Pakistan.

A samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan an saki damisar daga kejin da aka ajiye ta domin daukar bidiyon kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Dan TikTok da damuwa
Dan TikTok da damusa ta kashe. Hoto: The Rock
Source: Facebook

Blue News ta wallafa cewa an garzaya da Talha zuwa asibiti cikin mawuyacin hali, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

An kama mai gonar kiwon dabbobi

’Yan sanda sun kama mai gonar, mai suna Fayyaz, da kuma wani mai kirkirar bidiyo a TikTok mai suna Norman Hassan, bayan faruwar lamarin a yankin Kahna da ke Lahore.

Rahoton ya ce Hassan ne ya bukaci a saki damisar macen daga kejin da take domin a yi amfani da ita wajen daukar bidiyon.

Sai dai a lokacin daukar bidiyon ne dabbar ta yi tsalle ta afka wa Talha. Mahaifinsa da dan uwansa mai suna Hashim, wadanda su ma suke aiki a wajen, sun shaida harin.

Bayanin 'yan sandan Pakistan

’Yan sanda sun yi zargin cewa Hassan ya fara kokarin bayyana cewa kare ne ya raunata Talha, amma bincike ya nuna cewa damisa ce ta kai masa hari.

Kara karanta wannan

Yadda daliban jami'a 7 suka rasu ana tsaka da bikin kammala karatunsu

Bayan faruwar lamarin, rahoton the Mirror ya nuna cewa a halin yanzu, an mika damisar ga hukumar kula da namun daji domin ci gaba da bincike.

Jami’an tsaro na kuma binciken ko gonar kiwon namun dajin tana da lasisin da ya dace na ajiye irin wannan dabba.

Rundunar ’yan sandan Lahore ta tabbatar da kama mutanen biyu, inda ta ce jami’an ofishin ’yan sanda na Kahna ne suka gudanar da kamen.

Damusa a kulle
Wata damusa a kulle. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar rundunar, sha’awar yin bidiyon TikTok ba za ta taba zama mafi muhimmanci fiye da rayuwar dan Adam ba. Ta kuma ce za ta binciki duk wani sakaci da kuma kokarin boye gaskiyar abin da ya faru.

An yi harbe-harbe a Amurka

A wani labarin, mun rahoto cewa wani likita mai suna Matt Lambert, mai shekaru 55, ya harbe manajan wani gini a cikin dakin motsa jiki da ke Washington DC, babban birnin Amurka.

Bayan haka, ya gudu zuwa barandarsa, inda ya harbi wasu mutane hudu cikin 'yan mintuna. Daga bisani, ya kashe kansa yayin da yake cikin gidansa, bayan ya shafe lokaci yana tattaunawa da jami’an ’yan sanda ta waya.

Rahotanni sun nuna cewa Lambert na takaddama da shugabannin ginin kan matsalar danshi da ke cikin gidan da yake zaune a hawa na bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng