Wani dan shekara 26 ya kashe mahaifinsa don ya bashi kan kaza amma ya bawa ƙaninsa mai shekaru 7 sauran naman

Wani dan shekara 26 ya kashe mahaifinsa don ya bashi kan kaza amma ya bawa ƙaninsa mai shekaru 7 sauran naman

  • Matashi mai shekara 26 ya kashe mahaifinsa saboda ya umurci ya yankawa kaninsa kaza amma aka bashi kan kaza
  • Matashin ya ce ya fusata ne don mahaifinsu ya umurci ya yanka kaza don a bawa kaninsa
  • Ya ce abin da ya bashi haushi shine kan kazan kawai aka bashi yayin da kaninsa ya samu tsoka mai yawa

Ondo - Yan sanda a jihar Ondo sun kama wani mai shekaru 26, Godwin Mathew saboda kashe mahaifinsa, Mr Audu saboda ya bashi kan kaza.

A ruwayar Daily Trust, wanda ake zargin ya shaidawa yan sanda ya kashe mahaifinsa ne saboda ya bashi kan kaza amma ya bawa kaninsa wani sashi na kazan mai tsoka sosai.

Wani dan shekara 26 ya kashe mahaifinsa don ya bashi kan kaza amma ya bawa kaninsa mai shekaru 7 sauran naman
Taswirar Jihar Ondo. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

Mathew na daya daga cikin mutane 14 da yan sandan Ondo suka kama a watan Satumba bisa aikata laifuka daban-daban.

Kakakin yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce wanda ake zargin sun tafi gona da mahaifinsa a ranar 9 ga watan Satumba amma bai dawo gida tare da shi ba.

Daga bisani an gano matashin ya halaka mahaifinsa ne da adda.

Mai magana da yawun yan sandan ta ce Mrs Christiana Audu ce ta shigar da korafi game da lamarin a ofishin yan sanda na Ala a Akure.

Ta ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin.

Ya ce mahaifinsa ya umurce shi ya yanka kaza domin a dafa wa kaninsa mai shekaru bakwai.

A cewarsa:

"Amma, ni kan kazan kawai aka bani hakan yasa na kashe mahaifi na."

Odunlami ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu don yi masa shari'a.

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

A wani labarin, kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya yi alkawarin cewa majalisar jihar za ta cigaba da goyon bayan yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar da illar da hakan ke yi wa matasa da mazauna jihar.

A ruwayar The Punch, Obasa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, da kwamandan jihar, Ralph Igwenagu ya yi wa jagoranci.

Kakakin majalisar ya ce yana fatan idan aka hada hannu wurin yaki da matsalar hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar mutanen Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel