Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

  • Mudashiru Obasa ya ce bai yi mamakin ganin Legas ce kan gaba a bangaren ta'amulli da miyagun kwayoyi ba
  • Kakakin majalisar na Legas ya ce hakan ya faru ne saboda Legas gari ne da kowa daga jihohin Nigeria ke zuwa
  • A cewarsa, a cikin masu zuwan akwai na gari akwai na banza amma ya yi alkawarin za su cigaba da aiki don tsaftace jihar

Legas - Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya yi alkawarin cewa majalisar jihar za ta cigaba da goyon bayan yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar da illar da hakan ke yi wa matasa da mazauna jihar.

A ruwayar The Punch, Obasa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, da kwamandan jihar, Ralph Igwenagu ya yi wa jagoranci.

Read also

Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso gabas sun yanke hukunci na ƙarshe kan shugabancin 2023

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa
Kakakin Majalisar Jihar Legas, Mudashiru Obasa. Hoto: The Punch
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin majalisar ya ce yana fatan idan aka hada hannu wurin yaki da matsalar hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar mutanen Legas.

Ya ce bai yi mamakin yadda aka bayyana Legas a matsayin daya daga cikin matattaran 'yan kwaya ba a Nigeria, yana mai cewa hakan ba abin mamaki bane saboda yawan mutanen da ke shigowa Legas daga wasu jihohi.

A cewarsa:

"Ban yi bakin cikin ganin Legas ce jihar da ke kan gaba ba. Legas ta zama gidan kowa da kowa - na gari da na banza - kuma hakan ya zama kallubale ga gwamnati.
"Shi yasa yake da wahala gwamnatin Legas ta yi hasashe. Idan ka yi hasashe da wani adadin mutane a wannan shekarar, kafin ka sani, adadin mutane fiye da kashi uku na wanda ka lissafa sun shigo jihar.

Read also

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

"Shi yasa muke kokarin tallafawa gwamnatin tarayya ta hanyar bawa RRS kayan aiki. Mun kuma kafa asusun tsaro, da masu tsaro a unguwanni, da hukumar kula da cinkoson ababen hawa da wasu don kare rayuka da dukiyoyin mutane."

Ya kara da cewa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki na da muhimmanci domin matsalolin da ta'amulli da miyagun kwayoyi ke haifarwa na shafar kowa.

Martanin hukumar NDLEA kan lamarin

Tunda farko, Igwenagu ya mika godiyarsa ga majalisar Legas saboda shirya taron masu ruwa da tsaki inda ya ce ta taimaka wurin wayar da kan talakawa.

Ya ce jihar Legas na ta kallubale na ta'amulli da miyagun kwayoyi amma ya yi alkawari NDLEA za ta cigaba da aiki da majalisa don ganin an rage matsalar.

Source: Legit

Online view pixel