Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin 'yan Najeriya

Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin 'yan Najeriya

  • Hadimin shugaba Buhari, Femi Adesina, ya ce babu dan siyasa a mace ko raye da 'yan Najeriya ke so kamar Buhari
  • A cewarsa, babu shakka hatta Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da Aminu Kano ba su kai shugaban Buhari farin jini ba
  • Adesina ya ce mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo mutum nagari ne kuma mai tsabar gaskiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tara taron jama'a 'yan Najeriya fiye da fitattun 'yan siyasa kamar su Azikiwe, Obafemi Awolowo da Aminu Kano, kamar yadda Femi Adesina ya ce.

Duk da Awolowo, Azikiwe da Aminu Kanu sun rasu, sun cigaba da samun mutuntawa da girmamawa a ko ina, Daily Trust ta tabbatar.

Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin 'yan Najeriya
Adesina: Buhari ya fi Azikiwe, Awolowo da Aminu Kano farin jini wurin 'yan Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dukkansu sun taka muhimmiyar rawa wurin kwatar wa Najeriya 'yancin kan ta kuma tarihin kasar nan ba zai manta da su ba.

Kara karanta wannan

Shekara daya da rabi da Shugaba Buhari ya yi magana, har yau umarninsa bai fara aiki ba

Amma a rubutun Adesina na wannan makon, mai magana da yawun Buhari ya daidaita da tunanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na cewa Buhari ne ya fi kowanne dan siyasa farin jini.

A takardar, Adesina ya rubuta cewa, "Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo mutum ne nagari. Duk abinda ya fadi, ku dauke shi da muhimmanci.
"Akwai yuwuwar ka ce, toh me ake tsammanin mutum na biyu a kasa ya fadi game da shugabansa?
“Sai dai duk wanda ya yi aiki da Farfesa Yemi Osinbajo da Buhari, zai gane gaskiya. Mutum ne nagari kuma wanda ya dogara ga Ubangiji. Ba abun a mutu ko a yi rai ba ne, da ya zaba sai ya yi shiru game da halayen shugaban kasa."

Femi Adesina ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Duk wanda yace Buhari ya gaza tantirin makaryaci ne, Femi Adesina

"Ina da shekarun da ya dace in ce na ga abubuwa da yawa da kuma lamurran siyasa masu yawa. Na ga zamanin Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, Shehu Shagari, Aminu Kano, MKO Abiola, Bashir Tofa da sauransu.
"Amma ban taba ganin mutum mai irin jan hankali, daukar jama'a da farin jinin Muhammadu Buhari ba. A dukkan fadin kasar nan, arewa da kudu. Jama'a baibaye shi su ke kamar zuma."

Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku

A wani labari na daban, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta saka ranar 22 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa a matsayin ranar da za ta saurari karar da ke bukatar soke zaben Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, Daily Trust ta wallafa.

Kungiyar Incorporated Trustees of the Civil Society Observatory for Constitutional and Legal Compliance (CSOCLC) ta ce idan kotun ta aminta da bukatar ta, ta bada umarnin rantsar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin shugaban kasa tunda shi ne ya zo na biyu a zaben.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya bayyana abin da zai faru da masu neman hada Tinubu fada da Osinbajo

Kwamitin masu shari'a uku da ya samu shugabancin Mai shari'a Peter Ige, yayin sauraron, sun umarci cewa a mika takardun kotun gaban hukumar zabe mai zaman kanta, jam'iyyar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel