Duk wanda yace Buhari ya gaza tantirin makaryaci ne, Femi Adesina
- Hadimin Shugaban kasa yace Najeriya tafi tsaro yanzu fiye da 2015 da Buhari ya hau mulki
- Adesina yace Shugaba Buhari yayi kokari wajen cika alkawuran da ya yiwa yan Najeriya
- Shugaba Buhari ya yi alkawarin kammala wasu ayyukan da ya dauko
Abuja - Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa gwamnatin maigidansa bata gaza ba saboda tayi kokari a wasu wurare.
A hirar da yayi a shirin 'Politics Today' na ChannelsTV, Adesina yace duk wanda yace Shugaba Buhari ya gaza tantirin makaryaci ne.
Zaku tuna cewa Buhari ya dane mulki ne kan alkawura uku - Magance matsalar tsaro, yaki da rashawa, da kuma farfado da tattalin arziki.
Adesina yace a kan wadannan abubuwa uku, Buhari ya cika alkawuransa ga yan Najeriya.
Yace:
"Lallai akwai wuraren da akayi nasara, kuma akwai wuraren da ba'ayi sosai. Amma wani yace gaba daya mun gaza, wannan ba gaskiya bane."
"A wasu bangarorin za'a ga mutum bai yi kokari sosai ba. Da farko alkawura uku ne amma daga baya aka fadada zuwa tara."
Mai magana da yawun Buhari yace Najeriya ta fi tsaro yanzu fiye da lokacin da suka hau mulki a 2015.
Yace:
"Mun hau mulkin kasar nan babu tsaro; sai muka samar da tsaro. Amma daga baya sai abubuwa suka munana."
"Da farko matsalar yan ta'adda ne, sai kuma yan bindiga, masu garkuwa da mutane, dss. Rashin tsaro babban matsala ne."
Adesina yace gwamnatin maigidansa na iyakan kokarinta wajen samar da tsaro.
Buhari ya bayyana wasu nasarori 12 ya cimma a shekaru 2, wa'adin mulkinsa na biyu
Shekaru biyu cikin wa'adin mulkinsa na biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya lissafa nasarorin da ya cimma a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a wani taron ganawa da ministoci don tantance ayyukan gwamnatin sa.
Taron ganawar ya baiwa ministoci da shugabannin hukumomin dama su baje kolin ayyukansu don tantancewa tare da nuna ko sun dace da manufofin gwamnatin gaba daya.
Asali: Legit.ng