Sarakunan Arewa da Suka Nuna Turjiya ga Turawan Mulkin Mallaka a Najeriya
Fiye da karni guda da ya gabata, zuwan Turawan Birtaniya ya canza tarihi da tsarin rayuwa a ƙasar da ake kira Najeriya a yau.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayan mamaye Legas a shekarar 1861, Turawan suka fara shimfiɗa mulki, inda suka rika bi ta yankuna da dama har zuwa Arewacin ƙasar.

Source: UGC
Zuwan Turawa Arewacin Najeriya
A cewar masanin tarihi na Jami’ar Bayero, Dakta Abdullahi, Turawan sun shiga Najeriya ta hanyoyi uku: yawon bincike, yaɗa addinin Kirista, da kuma neman mulkin mallaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BBC Hausa ta rahoto Dakta Abdullahi yana cewa:
“Da farko sun zo ne suna kiran kansu a matsayin masu yawon buɗe ido da bincike, daga bisani kuma suka fara mallake yankuna.”
Wasu sarakuna sun karɓi Turawa cikin lumana, amma da yawa sun nuna masu turjiya, tare da kokarin kare ikon su da al’ummarsu.
Wannan rahoto ya zakulo fitattun sarakunan Arewacin Najeriya da suka tsaya kai da fata wajen kare mutuncin al’ummarsu daga Turawan mulkin mallaka.
Sarakunan da suka yi turjiya ga Turawa
1. Sarkin Musulmi Attahiru
Sultan Muhammadu Attahiru na farko shi ne Sarkin Musulmi na ƙarshe kafin Turawan mulkin mallaka su kwace Daular Usmaniyya.
Lokacin da Turawa suka fara mamaye Arewa a shekarun 1890, Attahiru ya jagoranci mayaƙansa wajen kare ikon Musulunci da yankinsa.
“Attahiru ya yi imanin cewa Musulmi ba su da izinin barin mulkinsu ga kafirai,” in ji Dakta Abdullahi.
Yaƙin da ya biyo baya ya tilasta masa barin Sakkwato, amma bai yi kasa a gwiwa ba — ya ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da aka kashe shi a wani gari da ke cikin jihar Gombe ta yanzu.
Mutuwarsa ta zama tamkar alamar ƙarshen Daular Usmaniyya da kuma farkon mulkin Turawa a Arewacin Najeriya.
2. Sultan Muhammadu Attahiru II
Bayan kisan Attahiru na farko, Turawa sun naɗa Muhammadu Attahiru II a matsayin sabon Sarkin Musulmi a 1903, suna fatan zai zama mai biyayya gare su. Amma akasin haka, shi ma ya nuna tsayin daka irin na mahaifinsa.
“Sun ɗora shi a kujera da niyyar samun amincewa, amma sai suka tarar da jarumin da bai yarda da mulkinsu ba,” in ji masanin tarihin.
Turawan sun ƙaddamar da farmaki a kansa bayan ya nuna rashin amincewa da dokokinsu, kuma daga bisani aka kore shi daga Sakkwato. Wannan ya tabbatar da cewa ikon Musulunci bai taɓa karɓar mulkin Turawa da gamsuwa ba.
3. Sarkin Kano Alu (Aliyu Babba)
Sarki Alu, wanda ake kira Aliyu Babba ko Alu Maisango, ya mulki Kano daga 1894 zuwa 1903. Shi ma ya shiga sahun manyan sarakunan da suka nuna turjiya ta zahiri ga Turawa.
A lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa Kano ne daga Sokoto, Sarki Alu ya samu labarin cewa Turawa sun shiga Kano abin da ya sa suka yada zango a Kwatarkwashi domin tattauna abin yi nagaba.
Amma ƙaddara ta riga fata: aka kama shi a kan hanyarsa ta zuwa Makka, inda Turawa suka tafi da shi zuwa Adamawa.
Dr. Raliya Zubair Mahmoud daga Kwalejin Kumbotso ta ce:
"Shi Sarki Alu ya kama hanya zuwa Gabas kuma jama'arsa suka bi shi domin guje wa Turawa to amma ƙaddara ta riga fata, inda ya haɗu da Turawa a kan hanyarsa ta zuwa Makka kuma sun kama shi suka tafi da shi inda suka kai shi Adamawa."
Tarihin Kano ya ɗauki Alu a matsayin sarki na ƙarshe da ya tsaya tsayin daka kafin Turawan su karɓi mulki da ƙarfi.
4. Shehun Borno, Mai Bukar Garbai
Shehun Borno, Mai Bukar Garbai, ya nuna jarumta ta musamman. Shi ne ɗaya daga cikin sarakunan da suka yi yaƙi da manyan ƙasashen Turai guda biyu lokaci guda — Birtaniya da Jamus.
“Yaƙin da Mai Bukar ya yi ya nuna cewa Borno na da cikakken tsari da sojoji kafin mamayar Turawa,” in ji Dakta Abdullahi.
Sai dai ƙarfin bindigogi da dabarun Turawa suka rinjayi mayaƙan Shehu, inda daga ƙarshe aka kashe shi a shekarar 1890.
Mutuwarsa ta zama alamar ƙarshen wata tsohuwar daula da ke cike da tarihi da daraja a arewacin Najeriya.
5. Etsu Nupe Abubakar
Etsu Abubakar, Sarkin Nupe, ya mulki daga 1897 zuwa 1901. Shi ma ya bijire wa shirin Turawa na kwace ikon kasuwanci da haraji.
A cewar Dakta Abdullahi, Turawa sun yi niyyar kafa tsarin haraji da tilasta ayyuka, amma Etsu Abubakar ya ƙi amincewa.
“Masarautar Nupe ta kasance cibiyar kasuwanci da sana’o’i, don haka Etsu ya yi imanin cewa tsarin Turawa zai lalata arzikin al’umma,” in ji masanin.
Bayan tsawon lokaci ana fafatawa, Turawa suka kwace ikon garin Bida, amma sun gaza cire darajar Etsu daga zukatan mutanensa.
Arewa ta Tsakiya: Jama'a sun ƙi miƙa wuya
A yankin Arewa ta Tsakiya — wato jihohin Nasarawa, Benue, Filato, Abuja — ma an samu turjiya daga kabilu da sarakunan gargajiya.
Misali, al’ummar Tiv da wasu kabilu na Bauchi sun yi bore tsakanin 1910 zuwa 1930 saboda tsarin haraji da aikin dole da Turawa suka kafa.
“Turawan sun nemi canza tsarin mulki da kasuwanci, amma mutanen yankin sun ƙi amincewa, suna kare martabar al’adunsu,” in ji Dakta Abdullahi.
Rahotanni dai sun nuna cewa turjiya ba ta tsaya a Arewa ba — ta mamaye sassan ƙasar baki ɗaya.
Hanyoyin da sarakuna suka bi wajen nuna turjiya
Masana tarihi sun bayyana cewa sarakuna sun yi turjiya ta fannoni huɗu:
- Ta makami – su da mayaƙansu sun yi amfani da kwari, baka da adduna yayin da Turawa ke amfani da bindigogi.
- Ta imani – da yawa sun ƙi amincewa da Turawa saboda dalilan addini.
- Ta tsarin mulki – sarakuna sun ƙi bin dokokin da suka saɓa tsarin gargajiya.
- Ta tattalin arziki – sun ƙi karɓar tsarin haraji da kasuwanci da Turawa suka tilasta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng



