Yusuf, Safinatu, Zahra da Sauran 'Ya 'Ya 5 da Buhari Ya Rasu Ya Bari a Duniya
Katsina - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga Yuli, 2025, ya bar yara goma daga auren da ya yi da mata biyu.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Asali: Twitter
Rahoto ya nuna cewa matarsa ta farko Safinatu Yusuf ta haifa wa Buhari 'ya'ya biyar, sannan matarsa ta biyu, Aisha Halilu, ita ma ta haifi 'ya'ya biyar.
A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bayani kan yaran Buhari da bayanan da aka samu game da karatu, aikinsu da rayuwar su, bisa rahotonnin manyan jaridu da WikiPedia.
Sai dai, Shugaba Buhari ya kasance mutum mai tsananin kare sirrin iyalinsa, don haka ba a samu cikakken bayani game da wasu daga cikin yaran nasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaran Safinatu Yusuf (1971–1988)
Safinatu Yusuf, matar farko ta Buhari, ta rasu a shekarar 2006. Ta haifa masa yara biyar, amma biyu daga cikinsu sun rasu sakamakon cutar sikila.

Asali: Twitter
1. Zulaihatu Buhari (Ta rasu)
Zulaihat "Zulai" Buhari Junaid (5 ga Disamba, 1972 – 29 ga Nuwamba, 2012) ita ce babbar 'yar Buhari da Safinatu. An san ta da tawali'u da nutsuwa, kuma waɗanda suke kusa da ita suna matuƙar sonta.
Ilimi
Ta fara karatunta a Amurka tun tana yarinya, sannan ta halarci Kwalejin Sojan Sama a Legas, daga baya kuma Queens College, Legas; ta kammala karatun sakandare a Kolejin Tarayya, Kaduna. Ta sami digiri na farko (B.Sc.) a fannin Tattalin Arziki da Difloma ta Digiri na Biyu (Postgraduate Diploma) a fannin Gudanarwa daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Aiki
Zulai ta yi aiki a bankin African Intercontinental, sannan daga baya ta yi aiki a Ma'aikatar Ma'adanai a Kaduna.
Ta kafa gidauniyar Hajiya Safinatu Buhari don tunawa da mahaifiyarta, inda take ba da agaji ga waɗanda cutar ciwon suga ta shafa.
Rayuwar Aure da Iyali
Ta auri Kyaftin Mahmud Junaid (mai ritaya), kuma ta kasance mace mai biyayya ga mijinta da kuma uwa ga 'ya'ya uku; manyan yara biyu da kuma jariri a lokacin mutuwarta.
2. Fatima Buhari
Haihuwa: An haifi Fatima Buhari a ranar 7 ga watan Maris, 1975.
Karatunta: Ta yi makaranta a makarantar firamare ta sojojin sama da ke Victoria Island, Lagos, sannan ta wuce kwalejin gwamnati ta Kaduna. Ta samu difloma daga Jami’ar Ahmadu Bello da kuma digiri na biyu daga jami'ar Stratford da ke Burtaniya.
Rayuwarta: Ta auri Bello Waziri Gwandu a shekarar 2003, kuma suna da 'ya'ya (jikokin Buhari).
Ayyukan Gwamnati: A shekarar 2021, an naɗa ta a matsayin memba a kwamitin gudanarwa na Cibiyar Ma'aikatan Shari'a ta Najeriya da Masu Binciken Zamba (CIFCFEN).
Mun ruwaito cewa an hango Fatima Buhari tana kuka sosai a Daura a ranar 15 ga Yuli, 2025, yayin shirye-shiryen jana’izar mahaifinta.
3. Musa Buhari (Ya rasu)
Shi ne ɗa namiji guda tilo da Buhari ya haifa da Safinatu. Shima ya rasu sakamakon cutar sikila. Ba a da bayanai kan rayuwarsa, inji rahoton Pulse.
4. Hadizatu-Nana Buhari
Hadiza Nana Buhari, ta yi karatu a makarantar First Essence International, sannan ta wuce Cobham Hall da ke Kent, Ƙasar Birtaniya, inji rahoton ThisDay.
Ta kuma yi karatu a Jami’ar Buckingham. Kafin hakan, ta samu ilimi a Cibiyar Koyar da Malamai ta Ƙasa, Kaduna, tare da samun digiri na biyu a fannin hulɗar ƙasashen duniya da dabarun tsare-tsare a Kwalejin Kimiyya ta Kaduna.
Hadiza Nana, ta auri tsohon ministan shari'a Abubakar Malami, a ranar 8 ga Yuli. An daura auren ne a cikin sirri a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, Abuja.
Hadiza ta kasance matar Abdulrahman Mamman Kurfi kafin su rabu, inda aurensu ya haifar da 'ya'ya guda shida. Yanzu Hadiza ita ce mata ta uku a gidan Abubakar Malami, inda Aisha ce matar farko, sai Fatima a matsayin ta biyu.
5. Safinatu Lami Buhari
Haihuwa: An haifi Safinatu Lami Buhari a ranar 13 ga watan Oktoba, 1983.
Karatunta: Ta halarci Essence International a Kaduna, daga nan ta wuce Cobham Hall a Kent, UK. Ta samu digiri daga jami'ar Plymouth sannan ta ci gaba da karatu a jami'ar Arden University, duk a Burtaniya.
Rayuwata: A 2019 ne muka ruwaito cewa Hajiya Safinatu wadda aka fi sani da Lami Buhari ta na auren Alhaji Abubakar Sama’ila Isa ne.
Abubakar Samaila Isa yana da ‘ya ‘ya biyu da ‘diyar shugaban kasar a wancan lokacin. ‘Ya'yan nasu su ne Isa (Khalifa) da kuma Isma’ila (Fahad).
Aiki: Tana aiki da kungiyoyin cigaban al’umma, inda take matsayin darakta a Africa Support & Empowerment Initiative (AFRISEI).
Yaran Aisha Halilu (1989– Zuwa yanzu)
Aisha Halilu Buhari, mace mai fafutukar kare haƙƙin mata da yara, ta haifi yara biyar da Buhari.
Ta kammala digiri a Public Administration daga jami'ar Ambrose Alli da kuma digirin digirgir a harkokin kasa-da-kasa daga NDA.

Asali: Twitter
'Ya'yan Aisha su ne:
6. Halima Buhari
Halima Muhammadu Buhari-Sheriff, da aka haifa a ranar 8 ga Oktoba, 1990, ita ce diyar farko ta tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Aisha Buhari. Lauya ce kuma fitacciyar mace.
Ilimi da aikin lauya:
Ta halarci International School Kaduna, sannan British School of Lomé, da Bellerby’s College a Brighton, da ke Birtaniya.
Ta samu digiri a fannin lauya daga Jami’ar Leicester, sannan ta halarci makarantar koyon lauya ta Najeriya inda ta samu lasisin aikin lauyanci a ranar 14 ga Yuli, 2016.
Yanzu haka lauya ce kuma ta yi aiki a matsayin mai gabatar da kara da mataimakiyar darakta a ma’aikatar shari’a ta jihar Borno.
Gwagwarmaya da karramawa:
Halima na da hannu a harkokin ci gaban mata da shari’a. A shekarar 2023, ita da 'yar uwarta Zahra sun karɓi lambar yabo daga NAWOJ a madadin mahaifiyarsu Aisha Buhari.
Rayuwar aure:

Kara karanta wannan
'Ba zan bar maku gadon dukiya ba,' Abin da Buhari ya fadawa ƴaƴansa kafin ya rasu
Halima ta auri Alhaji Babagana Muhammed Sheriff, attajiri daga jihar Borno, a wani bikin aure mai armashi da aka yi a shekarar 2012.
A jiya Talata, 15 ga Yulin 2025, bayan da aka binne gawar Muhammadu Buhari, mun ruwaito cewa Noor ta wallafa a shafinta na soshiyal midiya cewa:
"Zuciyata cike take da baƙin ciki saboda ba za mu samu damar ci gaba da kasancewa tare ba da kuma gudanar da abubuwan da na tsara mana ba.
"Zan ci gaba da tunaninka har abada. Ina addu’a Allah Ya ba ka matsayi mafi girma a Aljanna, kuma ruhinka ya huta cikin salama madawwami, Daddy."
7. Zahra Muhammadu Buhari
An haifi Zahra Muhammadu Buhari Indimi a ranar 18 ga watan Disambar 1994.
Karatunta: Ta yi karatu a Kaduna International da British School of Lomé a Togo. Ta kammala sakandare a kolejin Bellerby da ke Brighton, Burtaniya.
Ta samu digiri a fannin kimiyyar kwayoyin halitta daga jami'ar Surrey.
Rayuwarta: Zahra ta auri Ahmed Indimi a watan Disamba, 2016. Auren ya samu halarta manyan mutane da dama. Tana daga cikin yaran Buhari da aka fi saninsu a kasar.
Aiki: Tana harkar kasuwanci da ba da agaji, musamman ta hanyar Future Assured – shirin da mahaifiyarta ta assasa.
A matsayinta na kafa ACE Charity Africa, Zahra tana tallafawa yara masu fama da cutar sikila ta hanyar bayar da tallafin karatu, kafa sansanonin jinya da wayar da kai.
8. Yusuf Buhari
An haifi Yusuf Muhammadu Buhari a ranar 23 ga watan Afrilun 1992.
Karatunsa: Ya halarci Kaduna International da British School of Lomé da ke Togo. Ya kammala sakandare a kolejin Bellerby’s da ke Burtaniya, kuma ya samu digiri daga jami'ar Surrey a 2016.
Rayuwarsa: Ya auri Zahra Nasir Bayero, ‘yar Sarkin Bichi a watan Agusta 2021 – aurensu ya kafa tarihi a Najeriya.
Mun ruwaito cewa Yusuf Buhari ya taba tsira daga wani mummunan hadarin babur a 2017, wanda ya sa dole aka garzaya da shi Jamus neman magani.
9. Aisha Buhari
An haifi Aisha Buhari, watau Hanan a ranar 30 ga watan Agusta, 1998.
Karatunta: Ta yi karatu a Kaduna International. Sannan ta yi karatun digiri kan daukar hoto a jami'ar Ravensbourne da ke London.
Rayuwarta: Ta auri Mohammed Turad Sha’aban a 2020, kuma mun ruwaito cewa Hanan ta yi shagalin sunan danta Zayd a shekarar 2022.
Aiki: Hanan ta kafa wata gidauniya mai suna Hanan Buhari Foundation, wacce ke fafutukar kare matan da aka yi wa fyade da kuma kokarin dakile barnar.
10. Amina (Noor) Buhari
An haifi Amina Buhari a ranar 14 ga watan Satumba, 2004.
Karatunta: A 2017 tana makaranta a Kaduna International School. Za a iya cewa a 2025 ta kammala manyan makarantu.
Rayuwarta: Ita ce ƙarama a cikin yaran Buhari. Tana rayuwarta ne cikin sirri, ba tare da an samu bayani kan aurenta ko yara ba.
Manyan da suka tarbi gawar Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, filin jirgin Katsina ya cika da jama'a yayin da aka kawo gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga London.
Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima, da iyalai da 'yan uwan Buhari da kuma manyan jami'an gwamnati suka tarbi gawar.
An ce gwamnoni 20, ministoci, da shugabannin siyasa ne suka hallara a Daura, inda za a yi jana'iza tare da binne gawar Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng