Jerin sunayen 'ya'yan Buhari da makarantun da suka halarta

Jerin sunayen 'ya'yan Buhari da makarantun da suka halarta

John Paden, mawallafin littafin "Muhammadu Buhari: Kalubalen mulki a Najeriya" ya lissafa dukkan 'ya'yan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da makarantun da suka halarta tun daga firamare har zuwa jami'a.

1. Fatima: An haife ta a shekarar 1975. Ta halarci makarantar firamare ta 'ya'yan sojojin sama a Victoria Island, Legas. Ta halarci makarantar sakandire ta 'Government College, Kaduna. Ta yi karatun digiri na farko a jami'ar ABU, Zaria, kafin daga bisani ta wuce jami'ar kasuwanci ta Stratford da ke kasar Ingila inda ta yi digiri na biyu.

2. Nana Hadiza: An haife ta a shekarar 1981. Ta fara karatu a makarantar 'Essence International School da ke Cobham Hall, Kent, Ingila. Ta yi karatun jami'a a jami'ar Buckingham da ke kasar Ingila. Ta yi karatun diflomar malaman makaranta a Kaduna, sannan ta yi karatun digiri na biyu a 'Polytechnic Kaduna (KADPOLY)'.

3. Safinatu: An haife ta a shekarar 1983. Ta fara karatu a makarantar 'Essence International Schools; Cobham Hall, Kent, a kasar Ingila. Ta yi karatun digiri na farko a jami'ar Plymouth da ke kasar Ingila kafin daga baya ta koma jami'ar Arden da ke kasar Ingila domin ilimi mai zurfi.

4. Halima: An haife ta a shekarar 1990. Ta fara karatu a makarantar International Schools da ke Kaduna kafin daga bisani ta halarci British School Of Lome a kasar Ingila. Ta halarci makarantar 'Bellerby's College' da ke Brighton a kasar Ingila daga nan kuma ta wuce jami'ar birnin Leicester a kasar Ingila, sannan ta dawo gida Najeriya inda ta halarci makarantar horon lauyoyi da ke Legas.

DUBA WANNAN: Falmata Bulama: Iyaye da 'yan uwan matar aure sun juya mata baya saboda kubutar da mijinta daga kungiyar Boko Haram

5. Yusuf: An Haifa shi a shekarar 1992. Ya fara karatu a 'Kaduna International school, daga nan kuma ya wuce zuwa 'British school of Lome. Kazalika ya halarci makarantar 'Bellerby's College, Brighton' a kasar Ingila kafin daga bisani ya halarci jami'ar Surrey a kasar Ingila.

6. Zahra: An Haifa ta a shekarar 1994. Ta fara karatu a 'Kaduna International school, daga nan kuma ta wuce zuwa 'British school of Lome. Kazalika ta halarci makarantar 'Bellerby's College, Brighton' a kasar Ingila kafin daga bisani ta halarci jami'ar Surrey a kasar Ingila.

7. Aisha (Hanan): An haife ta shekarar 1998 kuma ta fara karatu a 'Kaduna International School'

8. Amina (Noor): An haife ta a shekarar 2004. Ta fara karatu a makarantar 'Kaduna international school'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel