Hotuna daga asibitin kudi da Yusuf Buhari ke kwance, bayan hatsarin babur
- A yanzu haka Yusuf Buhari na samun kulawa a asibitin Cedarcrest dake yankin Gudu, Abuja
- Dan shugaban kasar ya samu ranunuka, bayan hatsari da yayi akan babur a daren ranar Talata
- An gano jami’an tsaro a wajen asibitin yayinda Yusuf ke samun kula a asibitin
Bayan hatsari da yayi akan babur, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, na jinya a asibitin Cedarcrest dake yankin Gudu, Abuja
A bisa hotunan dake yawo a shafukan yanar gizo, an gano jami’an tsaro a wajen asibitin, yayinda dan shugaban kasar ke samun kula a asibitin.
Legit.ng ta lura cewa babu cunkoson mutane dake shiga asibitin da dan shugaban kasar ke jinya sannan kuma ga dukkan alamu abubuwa na gudana yadda ya kamata.
Kalli hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Dan shugaba Buhari ya yi hatsari da babur
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng