Labarin Hajiya Safinatu Buhari mai auren Abubakar Samaila Isa

Labarin Hajiya Safinatu Buhari mai auren Abubakar Samaila Isa

Yayin da Hajiya Zahrah Buhari ta fito ya bayyana cewa ba ta iya Hausa sosai ba, mun kuma samu labarin wata ‘Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda mutane da-dama ba su sani ba.

Jaridar Katsina Post ta kawo labarin Safinatu Muhammadu Buhari wanda ‘Diya ce wurin shugaban kasar. Tsohuwar Mai dakin shugaban kasa Buhari, Marigayiya Safinatu ce ta haife ta.

Hajiya Safinatu wanda a kan kira Lami Buhari ta na auren Alhaji Abubakar Sama’ila Isa ne. Ana zagin cewa Abubakar Sama’ila Isa ya na takun-saka da gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari.

Kwanakin baya dai Mai girma gwamnan ya fito ya na nuna cewa akwai wasu ‘yan siyasar jihar masu zama a Abuja da ke kokarin kawowa jam’iyyar APC da gwamnatinsa cikas a jihar Katsina.

KU KARANTA: Abin da ya sa ban iya Hausa rangadau ba - Zahra Buhari

Safinatu Buhari ita ce ‘Diyar shugaban kasa Buhari ta biyar da aka haifa masa. Wannan Mata ta na cikin ragowar ‘ya ‘ya ukun Marigayiyar Mahaifiyarsu wanda aka sanyawa sunanta a Duniya.

Kamar yadda mu ka samu labari, ‘Yanuwan Lami su ne Zulaihatu, Fatima, Musa da Nana Hadiza. Sai dai Musa da Zulaihatu wanda ita ce babbar ‘diyar shugaban kasar sun rasu a shekarun baya.

Katsina Post ta ce Abubakar Samaila Isa ya na da ‘ya ‘ya biyu da ‘diyar shugaban kasar. ‘Ya ‘yan na su su ne Isa (wanda ake kira da Khalifa) da kuma Isma’ila wanda ake yi wa lakabi da Fahd).

Matashin ‘Dan siyasar ya sa wa ‘ya ‘yan na sa sunayen Mahaifinsa ne da kuma Kakansa. Abubakar Sama Isa dai babban ‘dan kasuwa ne kuma Aminin shugaba Buhari tun da dadewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel