Hotuna daga bikin Zahra Buhari

Hotuna daga bikin Zahra Buhari

Zahra na ci gaba da tafiyarta na komawa Zahra (Buhari Indimi tare da wani kwallon aure da akayi don girmamawa ga ma’auratan a daren ranar Laraba.

Hotuna daga bikin Zahra Buhari
Zahmed2016

A wasu yan makonni da suka wuce kafofin watsa labarai sun zo da labaran dakatar da auren tsakanin yar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga dan biloniya Mohammed Indimi Ahmed.

Da farko ya kasance baiko tare da akwatunan biliyoyin naira sannan kuma bikin wankan Amarya da akayi a ranar Talata, duk a shirye-shiryen auren da za’a daura a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Zahra Buhari tayi tsadaddan taron wankan Amarya

A ranar Laraba, ma’auratan da akayi wa baikon sunyi wani tsadadden taro, wanda ya samu halartan abokai makusanta. Anyi taron ne a Royal Wedding Hall, Dunes Centre, Maitama, Abuja. Shugaban kasa da matarsa basu halarci taron ba.

Abunda suka sa

Hotuna daga bikin Zahra Buhari
Yayan Zahra, Yusuf (a tsakiya) tare da abokansa a gurin kwallon.

A gurin hadadden taron, angwanen sun sanya kaya kalar afarari yayinda amare suka sanya dogayen riguan farko daga Elie Saab sannan na biyu daga Huddaya, mai zane surukar Maryam da Sani Abacha.

Kwaliyyar taron bikin ya kasance da furanni kalar afarari sannan kuma aka shirya gurin kayan sha tare da manyan kofuna na kaloli daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin kudin 2017

Bakin da suka halarci gurin, ya nuna cewa yayan masu kudi da kuma shahararrun masu nishadantarwa a Najeriya.

Wadanda suka tafiyar da taron sune mawaki Dare Art Alade da kuma mai barkwanci AY. Waka kuma ya fito daga Dija, Adekunle Gold, Seyi Shay, Kiss Daniel da kuma Jimmy Jatt da sauransu. Sanatan barkwanci na Abuja ya kasance a matsayin bako.

Hotuna daga bikin Zahra Buhari
Mai zane, Hudayya (a dama) da wata bakuwa a gurin taron

Manyan masu tsaron taron sun bukaci baki da su ajiye wayoyinsu da sauran abubuwa a kofar shiga. An rahoto cewa sugaban kasa sha’awar binciken jama’a kewaye da babban ranar yarsa kuma zai fi so a hana haka ta ko wani hali.

Hotuna daga bikin Zahra Buhari
Wata bakuwa a gaban “coat of arms” din ma’auratan

A cewar wani labari, ana zargin an hana kannen ango mata shiga taron kamar yadda suke da alhakin sakin hotunan baikon.

Zuwa yanzu babu wani hoto da suka saki da kansu amma ku saurari bayani daga Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel