Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Halima diya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari

- Matashiyar mai shekaru 30 a duniya ta samu ingantaccen ilimi har zuwa matakin lauya

- Bayan kammalar karatunta, ta aura mijinta Alhaji babagana Sheriff dan asalin jihar Borno

Halima irin matannan ne da ake kwatantawa da 'kyau ga kwakwalwa'. Ta na da kyakkyawar sura, kwarjini ga kuma digiri a fannin shari'a.

An haifi Halima Buhari a ranar 8 ga watan Oktoba 1990, wadda yanzu haka shekarunta 30 da haihuwa. Halima cikakkiyar 'yar Najeriya ce, kuma mata ce ga Babagana Sheriff.

Halima diya ce ga Aisha da Muhammadu Buhari wanda yake mulkar Najeriya tun shekarar 2015. Mahaifinta yayi murabus ne a matsayin shugaban kasa na mulkin soja a shekarar 1983 zuwa 1985.

Tayi jami'o'i har guda 4. Mahaifiyar ta ce matar shugaban kasan Najeriya. Aisha Buhari babbar 'yar kasuwa ce, kamfanin gyaran jikin mata na 'Hanzy Spa', mallakinta ne.

Sannan ita ce shugabar cibiyar Hanzy Beauty, da kuma wurin gyaran jikin mata dake Kaduna da Abuja.

Halima tana da 'yan uwa 9, 5 daga auren mahaifinta na farko da matarsa marigayiya Safinatu, sai kuma 4 wadanda suke uwa daya uba daya.

Biyar din da suke uba daya sun hada da Zulaihat ( marigayiya), Fatima, Musa ( marigayi), Hadiza da Safinatu.

Sauran 4 da suke uwa daya uba daya, sun hada da Aisha, Yusuf, Zahra da Amina.

Zulaihat ta rasu a watan Nuwamban 2012 sakamakon fama da cutar sikila bayan ta haihu. Musa cutar sikila ce tayi ajalinsa.

Halima tayi karatu mai zurfi, kamar yadda 'yan uwanta suka yi. Ta yi makarantu da dama kamar: Kaduna British School of Lome, Bellerby's College dake Brighton, sai jam'ar Leicester dake Ingila da makarantar Shari'a ta Ingila.

Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hoto daga Halima Buhari
Asali: UGC

An rantsar da Halima a matsayin cikakkiyar lauya a wani taro na 2016 a Abuja. Mahaifiyarta da 'yan uwanta, Yusuf da Zahra sun je mata babban taron. Yanzu haka kyakkyawar matar na aiki a matsayin lauya.

Halima ta auri mijinta, Alhaji Babagana Muhammed Sheriff bayan soyayya mai tsawo da suka yi. Cikakken dan jihar Borno ne.

Anyi gagarumin shagalin aurensu, a lokacin aurenta wanda duk 'yan Najeriya suka yi ta mata sambarka.

KU KARANTA: Dakarun soji sama sun ragargaji 'yan bindigar daji a Kaduna

Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hoto daga Halima Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

Limamin masallacin Juma'an Yahaya Road ne ya daura auren. Manyan mutane kamar Mahaifinta, Buhari, Sanata Kanti Bello, Janar Buba Marwa da gwamnonin jihohi kamar na Kano, Borno, Kaduna da kuma mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, duk sun halarci daurin auren, don haka aka tsananta tsaro a lokacin gagarumin taron.

Halima Buhari na cikin kyawawan yaran shugaba Muhammadu Buhari. Duk da nasabarta, arziki da daukakar danginta, ta jajirce wurin yin ilimi mai zurfi don samun rufin asiri. Tana daya daga cikin lauyoyin da kasar nan ke ji da su.

Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Cikakken tarihin Halima Buhari Sheriff, diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Hoto daga Hausaroom
Asali: UGC

A wani labari na daban, Precious Chikwendu, ta tabbatar da mutuwar aurenta da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode.

Matar mai yara 4, ta sanar da mutuwar auren nata bayan ta wallafa hotunan yaranta a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Wani mabiyin ta na Instagram yayi tsokaci a karkashin hoton da ta wallafa, "Aurenki na lalacewa, amma wadannan yaran naki basu saka miki karfin guiwar komawa garesu ba. Na tausaya miki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng