Waiwaye: Labarin Safinatu, matar Shugaban Kasa Buhari ta farko

Waiwaye: Labarin Safinatu, matar Shugaban Kasa Buhari ta farko

Legit.ng ta waiwaya domin zakulo muku tarihin Malama Safinatu, matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta farko, wadda ta aure shi auren saurayi da budurwa, tana da shekaru 18 da haihuwa, sannan ta rasu tana da shekara 53 a duniya, Allah ya rahamshe ta.

An dai haifi Hajiya Safinatu ranar 11 ga watan Disambar 1952 a garin Jos. Mahaifinta Alhaji Yusuf Mani ya haifi ‘ya’ya 13. Su 7 ne 'ya'ya wajen mahaifiyarta Hajiya Hadizatu Mani. Safinatu baffulatana ce, 'yar asalin garin Mani a Jahar Katsina.

Ta yi karatun boko da na addini wanda yasa ta kware a bangaren larabci.

A shekarar 1966, tana da shekara 14 ta hadu da mijinta Buhari a karo na farko yana soja. Zuwansa gidansu tare da marigayi Shehu Musa ‘Yar'adua don ganawa da mahaifinta da yake aiki a Legas a matsayin Sakatare na Alhaji Musa ‘Yaradua.

Labarin Safinatu, matar Shugaban Kasa Buhari ta farko
Labarin Safinatu, matar Shugaban Kasa Buhari ta farko

Buhari ya cigaba da zuwa gidansu Safinatu don soyayyar da ya fara yi mata. Haduwar su ba dadewa aka fara yakin basasar Biyafara wanda ya sa Buhari ya tafi sansanin yaki ya bar Safinatu cikin kewarsa. Cikar ta shekara 18 a duniya aka daura musu aure.

Bayan auren su suka koma gidan Gwamnati a Legas ranar 19 ga watan Janairu, 1984, a lokacin Buhari ya zama Shugaban Kasa na mulkin soja, inda ya tumbuke mulkin farar hula, tare da aikin su janar Abacha da IBB.

Safinatu mutum ce mai shuru-shuru, bata cika yawan magana ba, hakan ya sa, da yawa mutanen Najeriya basu san labari sosai a kan ta ba, duk da tana matsayi na matar shugaban kasa. Tafi maida hankali ne a kan kula da gidanta da ‘ya’yanta. Bata cika shiga harkar shugaban a mulki ba, amma ta kan sauki baki a gidan ta.

Sau da kuma shi migidanta Buhari zai karya da abokan aikinsa ne. Hakan ma dare yakan tsaga amma baki a gidan basu watse ba, wanda zai sa sukai har tsakar dare basuyi bacci ba a Dodan Baracks din.

Kafin hawan Buharin dai mulki a lokacin, takan ce yana da lokaci ga iyalin shi amma bayan hawansa mulki ya sa rasa lokaci. Domin a da, shi zai tuka su daga Jos zuwa Daura da Kaduna ma, amma bayan hawansa mulki hakan ya gagara..

A lokacin da suka hau mulki, bayan da tattalin arzikin kasa yayi kasa, a lokacin ana Buhariyya ta farko, ta kai har su kan su iyalin shugaban kasar sun shiga matsalar kudi. Har sai daya kai Haj. Safinatu ta sayar da motar ta don biyan wasu bukatunta dana ‘ya’yanta.

A duk lokacin dafa abinci, ita take dafawa da hannunta da taimakon hadimanta. A maimakon yadda matan manya kan manta da girki, da zarar sun sami gwamnati.

Hasali ma, uwar gida Safinatu, tafi dafa abincin gargajiya, irin wanda shi maigidan nata yafi so, irinsu Farfesu da fura, da ma kayan taba ka lashe, irinsu dashishi da alkubus. Shugaban yana son tuwon shinkafa da miyar taushe ko agushi. Abincin dare kuma basu cika mai nauyi ba, sai hadawa da kayan itatuwa.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta fadi wa zai lashe zaben 2019

Ta haifi ‘ya’ya hudu : Zulaihatu ( Marigayiya), Fatima, Hadiza da Musa ( Marigayi). A 1980 dai aurensu ya mutu, a dalilin karbar tallafin kudi da tayi daga gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida lokacin da mijinta yake kulle. Sai daga baya, a 1989 Buhari ya auri matarsa ta biyu Aisha.

A 1988 ne dai Malama Safina ta kamu da ciwon siga, wato dayabetis, wanda ya kamata a Saudiya, tayi jinyar tsawon shekara takwas. Ta rasu a ranar 14 ga watan Janairu, 2006 tana da shekara 53.

Darasi daga rayuwarta:

Kafin rasuwarta, Malama Safinatu tace; ‘muhimmin abu ne a wajen matar shugaban kasa tayi hakuri da mutane da mijinta da canjin da zasu samu yayin da suka hau mulki’.

'Matan Shugabn Kasa ya kamata a dinga basu damar Magana akan muhimmancin kasa da zama Uwa ga mutanen Kasa.'

Allah ji kan Malama Safinatu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel