Takaitaccen tarihin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki

Takaitaccen tarihin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki

A yau 19 ga Watan Disamba ne Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya cika shekaru 56 a Duniya. Legit Hausa ta kawo maku wasu manyan abubuwa a game da rayuwar babban ‘Dan Majalisar Kasar a daidai wannan rana.

Takaitaccen tarihin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki

Yau ne Bukola Saraki ya cika shekaru 56 da haihuwa
Source: Instagram

1. Haihuwa

An haifi Bukola Saraki ne a Ranar 16 ga Watan Disamban 1962, kenan a yau Laraba ne Sanatan na Jihar Kwara ta tsakiua ya cika shekaru 56 cir a Duniya. Sunan Mahaifin sa Sanata Olusola Saraki, Mahaifiyar sa kuma ita ce Florence Morenike Saraki.

2. Karatu

Abubakar Bukola Saraki ya bar Najeriya ne zuwa Kasar Ingila inda yayi karatun ilmin likitanci a wata Jami’a da ake ji da ita a Turai. Saraki yayi karatun sakandaren sa ne a makarantar Corono da kuma Kings’ College har zuwa shekarar 1978.

3. Aikin banki

A waje Saraki ya soma aiki a matsayin Malamin lafiya kafin ya tattara ya dawo gida. Duk da cewa Bukola Saraki Likita ne, ya shiga harkar banki ne bayan dawowar sa Najeriya inda ya rike bankin nan na Societe General bank daga 1999 zuwa 2000.

4. Aiki da Gwamnati

Bayan kafuwar Gwamnatin Olusegun Obasanjo ne Bukola Saraki ya zama mai ba shugaban kasar shawara a kan harkokin kasafin kudi. A lokacin da Saraki yake aiki a fadar Shugaban kasar ya kawo wasu tsare-tsare da su ka shafi tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Shugaban Majalisar Tarayya yace zaben Buhari a 2019 zai haifar da matsala

5. Siyasa

A 2003 ne Bukola Saraki ya shiga cikin harkar siyasa tsundum inda ya zama Gwamnan Jihar sa ta Kwara. Saraki ya zarce a kan mulki a 2007 har ta kai ya zama shugaban Gwamnonin Kasar. Saraki bada karfi a bangaren wutan lantarki da noma da kiwon lafiya.

6. Majalisa

A 2011 ne Saraki ya gaji ‘Yar uwar sa Gbemisola Saraki a matsayin Sanata inda ya rike kujerar da Mahaifin su ya rike daga 1979 zuwa 1983. A wancan lokaci, Sanatan yana cikin wadanda su kayi ta babatu game da barnar da ke cikin tsarin tattafin man fetur.

7. Shugaban Majalisar Dattawa

A 2014 ne Bukola Saraki da wasu manyan ‘Yan PDP su ka sauya sheka zuwa APC. Bayan ya lashe zabe a 2015 ne ya nemi kujerar shugaban majalisar dattawa. Saraki yayi nasara duk da Jam’iyyar sa ta APC mai mulki ba ta ji dadi ba a wani zabe da ya zo da ce-ce-ku-ce ba.

8. Rikicin kujerar Majalisa

Bayan hawan Saraki kan kujera ne aka rika shari’a da shi a Kotu inda ake zargin sa da laifin kin bayyana kadarorin sa da kuma wasu laifuffuka na wawurar dukiyar Gwamnati a lokacin yana Gwamna a Jihar Kwara. A karshe Kotun loki da wanke Sanatan bayan an yi ta sa-in-sa.

9. Komawa PDP da takara

A cikin 2018 ne Bukola Saraki ya sake tattarawa ya koma PDP bayan wasu Sanatocin kasar sun sauya-sheka daga APC. Saraki ya nemi takarar Shugaban kasa a PDP inda ya zo na 3 a zaben fitar da gwani. Daga baya Saraki ya koma Darektan yakin neman zaben Atiku wanda yayi nasara.

10. Iyali

Bukola Saraki yana auren Toyin Saraki wanda ta haifa masa ‘Ya ‘ya har 4. Daga cikin ‘Ya ‘yan akwai Halima Oluwatosin Saraki wanda tayi aure a 2017. Bukola Saraki ya rike sarautar Turakin Ilorin a Jihar sa ta Kwara kafin ayi masa nadin Wazirin Garin Ilorin a cikin shekarar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel