Karin Albashi: Kungiyar TUC Ta Ba 'Yan Najeriya Tabbaci Kan Hauhawan Farashin Kaya, Ta Fadi Dalilai

Karin Albashi: Kungiyar TUC Ta Ba 'Yan Najeriya Tabbaci Kan Hauhawan Farashin Kaya, Ta Fadi Dalilai

  • Yayin ake neman tsayar da mafi karancin albashi a Najeriya, kungiyar TUC ta ba 'yan kasar tabbaci kan farashin kaya
  • Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo shi ya bayyana haka inda ya ce karin ba dole ya kara farashin kayayyaki ba a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu jihohi suka kara mafi karancin albashi yayin da aka yi bikin ranar ma'aikata a jiya Laraba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta TUC ta magantu kan karin mafi karancin albashi a Najeriya.

Kungiyar ta ba da tabbacin cewa karin kudin ba zai kara hauwahan farashin kaya ba a kasar.

TUC ta magantu kan karin albashi da tasirin hakan ga farashin kaya
Kungiyar TUC ta ce karin albashi ba zai taba kara farashin kaya ba. Hoto: Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress.
Asali: Twitter

TUC ta bukaci karin albashin ma'aikata

Kara karanta wannan

Ranar ma'aikata: Tinubu ya yafewa masu tafiya a jirgin kasa kudin sufuri na kwana 4

Shugaban kungiyar, Festus Osifo shi ya bayyana haka ne yayin hira da Channels TV a jiya Laraba 1 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osifo ya ce karin mafi karancin albashi ya halatta ganin yadda jihohi suka kara samun kudin shiga daga Gwamnatin Tarayya.

"Idan ka duba yanzu, daga watan Mayun 2023 kudin da Gwamnatin Tarayya ta ke ba jihohi ya ninku sau uku."

- Festus Osifo

TUC ta yi magana kan farashin kaya

"Wannan shi ya ke nuna jihohi suna da kudi da za su gina makarantu da hanyoyi da sauransu."
"Wannan karin albashi da ake magana ba zai kara farashin kaya ba saboda ko ba a ba ma'aikata ba dole za a kashe su ta wasu fannonin."

- Festus Osifo

Osifo ya ce karin kudi ga ma'aikata ba dole ba ne ya kara hauhawan farashin kaya da ake fuskanta a yanzu.

Kara karanta wannan

Kwana 7: kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnati wa'adin janye karin kudin wuta

Gwamna Otu ya kara albashin ma'aikata

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar jiharsa.

Gwamnan ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan domin rage musu radadin da suke ciki musamman halin kunci.

Otu ya ce sun amince da karin albashin ne duba da halin da jihar ke ciki na rashin kuɗi inda ya yi alkawarin ci gaba da kula da walwalar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel