Ranar Ma’aikata: Tinubu Ya Yafewa Masu Tafiya a Jirgin Kasa Kudin Sufuri Na Kwana 4

Ranar Ma’aikata: Tinubu Ya Yafewa Masu Tafiya a Jirgin Kasa Kudin Sufuri Na Kwana 4

  • Gwamnatin tarayya ta ayyana cewa za a yi kwana hudu ana amfani da jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Aba kyauta
  • Ministan sufuri na kasa, Sa'idu Ahmad Alkali ne ya bayyana haka yayin kaddamar da jirgin kasan a garin Fatakwal
  • Ministan ya kuma bayyana irin matakin da za a dauka domin ganin farashin tiketin jirgin kasa ya sauka a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Port harcourt, jihar Rivers - A yunkurin ta na saukakawa al'umma, gwamnatin tarayya ta ayyana cewa za a yi amfani da jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Aba kyauta.

Bola Tinubu
Jirgin kasan Fatakwal zuwa Aba ya fara aiki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jigilar kyautar za ta kasance na kwana hudu a kan titin jirgin wanda yake da nisan kilomita 62, daga 1 zuwa 4 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Kwana 7: kungiyoyin kwadago sun bawa gwamnati wa'adin janye karin kudin wuta

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar sufuri ta kasa, Muhammad Tahir Zakari ne ya bayyana hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jami'in, ministan sufuri, Sa'idu Ahmad Alkali ya bada sanarwar tabbacin hakan yayin kaddamar da jirgin kasan a garin Fatakwal.

Kokarin gwamnatin Tinubu kan sufuri

Ministan ya bayyana cewa harkar sufuri na daya daga cikin abubuwan da shugaba Bola Tinubu ya bawa muhimmanci.

Ya kuma mika godiya ga shugaban kasar bisa yadda ya goyi bayan aikin har aka tabbatar da kammala shi a kan lokaci.

Alfanun da za a samu a tashar jirgin

A cewarsa, kammala aikin jirgin kasan zai kara bunkasa harkar tattalin arziki a yankin dama Najeriya baki daya, cewar jaridar Punch.

Sannan ya bayyana yadda ake shirin kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri wanda zai bi ta garuruwa da dama domin bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

Kokarin gwamnati kan rage farashin tiketi

Akan maganar farashi kuma, ministan ya ce a halin yanzu suna duba yiwuwar sauya mai din da jirgin ke amfani da shi wanda hakan zai kawo saukin farashin tiketi.

A yayin bikin kaddamar da jirgin kasan, ministan ya samu rakiyar manyan jami'ai daga ma'aikatar sufuri ta kasa tare da sarakunan gargajiya.

An dakatar da ayyuka a filin jirgin saman Legas

A wani rahoton, kun ji cewa, gobara ta tashi a bangaren filin jiragen saman Murtala Muhammad (MMIA) da sanyin safiyar Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta dauki matakin karkatar da dukkanin ayyukan jiragen sama daga bangaren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel