Kyakkyawar Budurwa Mai Hannu Daya Ta Dauki Hankula Sosai a Intanet

Kyakkyawar Budurwa Mai Hannu Daya Ta Dauki Hankula Sosai a Intanet

  • Wata kyakkyawar budurwa mai hannu ɗaya ta yi suna a manhajar TikTok saboda tsananin kyawun da take da shi
  • Budurwar mai suna Akosua Joyce, ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna kyawunta inda mutane da dama suka yi ta yabon kyawun na ta
  • Masu amfani da TikTok da dama da suka kalli bidiyon Akosua sun garzaya sashen bayani inda suka yaba da kyawunta

Masu amfani da TikTok sun yaba da kyawun wata kyakkyawar budurwa mai hannu ɗaya.

Kyakkyawar budurwar mai suna Akosua Joyce, ta sanya bidiyo a TikTok inda ta nuna tsabagen kyawunta domin mutane su gani.

Budurwa mai hannu daya ta dauki hankula
Bidiyon kyakkyawar budurwar ya dauki hankula Hoto: TikTok/@akosua_joyce
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, an nuna Akosua akan wani titi inda ta nuna dirin da take da shi ta hanyar juya baya tana tafiya cikin rangwaɗa.

Nan da nan mutane suka lura da cewa hannu ɗaya kawai gare ta, amma hakan bai rage mata komai ba a kyawun da take da shi.

Kara karanta wannan

"Ta Yi Kuskuren Cika Masa Tanki": Rigima Ta Kaure Tsakani Wani Da Dan Najeriya Da Mai Zuba Man Fetur, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hannunta na hagu bai cika ba, inda ya yi kama da kamar an yanke shi, amma duk da haka kyawunta bai ragu ba.

Kyakkyawar budurwa mai hannu ɗaya ta yaɗu a TikTok

Shafin Akosua na TikTok cike yake da bidiyoyinta wanda ta nuna kyawunta sannan ba ta taɓa ɓoye nakasar da take da ita ba.

Mutane da dama ta shiga ransu saboda yadda ta ɗauki rayuwa ba da zafi ba duk da lallurar da take da ita.

Nan da nan waɗanda suka yi kaciɓus da bidiyon suka garzaya sashen bayani domin yaba wa da kyawun da take da shi.

Menene ƴan TikTok ke cewa kan bidiyon?

@ibraheemmusefiuol ya rubuta:

"Allah zai ci gaba da yi miki albarka."

@Samson enefiok ya rubuta:

"Wow! Kina da kyau sosai."

@Teemoney ya rubuta:

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim Din Kannywood Ya Gamu Da Babbar Jarabawa, Ya Nemi a Taimaka Ma Sa

"Kina da matuƙar kyau sosai."

@zrarcafe ya rubuta:

"Na yaba da jajircewarki, kina da kyau sosai."

Kyakkyawan Kurma Ya Koka Kan Rashin Budurwa

A wani labarin kuma wani kyakkyawan kurma ya koka kan halin da ys tsinci kan shina ciki a sakamakon lallurar da yake fama da ita.

Kurman ya yi nuni da cewa duk da kyawun da yake da shi, samun budurwa ya zama babban jan aiki a wajensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel