Budurwa 'Yar Najeriya Ta Samu a N245k a Sabon Shirin Da Twitter Ta Bullo Da Shi

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Samu a N245k a Sabon Shirin Da Twitter Ta Bullo Da Shi

  • Wata budurwa ta amfana da shirin raba kuɗin shiga da aka samu ta hanyar talla a Twitter wanda Elon Musk ya kawo
  • Budurwar mai suna, Bamidele, ta sanya hoton yawan kuɗin da ta samu inda ta ce su ne aka fara biyanta
  • Bamidele da wasu masu amfani da Twitter da suka cika sharuɗɗan, za su riƙa samun kuɗaɗe a manhajar wacce yanzu aka sani da sunan X

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ƴar Najeriya ta samu sama da N245k a shirin raba kuɗin tallan da aka samu a Twitter wanda Elon Musk ya kawo.

Budurwar mai suna Bamidele, ta sanya hoton ƙididdigar kuɗin da ta cancanci Twitter wacce yanzu aka sani da X, za ta biya ta.

Budurwa ta samu N245k a Twitter
Budurwa ta samu N245k a sabon shirin Twitter Hoto: Getty Images/Worawee Meepian, Bloomberg and Twitter/@nihiinn. Hoton budurwa an yi amfani da shi ne kawai domin misali
Asali: UGC

Bamidele tana da masu bibiyarta har 102.5k, sannan ta cancanci ta samu N491k a Twitter amma a yanzu N245k kawai za ta iya cirewa.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Samu Kyautar N500k, Ta Duka Kan Gwiwoyinta Tana Godiya Ga Wanda Ya Yi Mata Kyautar

Ta bayyana cewa wannan shi ne karon farko da Twitter za ta biya ta kuɗin tun lokacin da Elon Musk ya kawo shirin a watan Yuli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Twitter ta biya ƴar Najeriya N245k

Masu amfani da Twitter da dama waɗanda suka ga hoton yawan kuɗin da aka biya ta, sun taya ta murna sosai.

Domin samun damar shiga tsarin dole sai an cike wasu sharuɗɗa ciki har da samun mutum miliyan biyar waɗanda suka ga wallafar da mutum ya yi a Twitter cikin watanni uku.

Haka kuma dole sai ya shiga tsarin Twitter Blue, kuma yana da aƙalla mabiya 500.

Martani ƴan soshiyal midiya

@Tony_of_lagos ya rubuta:

"Turo min 200k."

@HaYoMiDe_ ya rubuta:

"Nima nawa suna kan hanya."

@JJames_066 ya rubuta:

"Ki cigaba da jajircewa akwai amfanin yin hakan."

Kara karanta wannan

"Dole Sai Ka Kashe N17m": Matashi Ya Soke Aurensa Da Budurwarsa Saboda Ta Bukaci Sai An Yi Biki Na Kece Raini

@Big_Yem ya rubuta:

"Lallai kina shagalinki."

@_kingjonah ya rubuta:

"Kina shagalinki, ni ban ga komai ba. har yanzu."

Banki Ya Yi Kuskuren Biyan Kwastomomi Kudi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani banki a ƙasar Ireland ya yi kuskuren batin mutane su riƙa cirar kuɗi kyauta.

Kwastomomin bankin dai sun riƙa cirar kuɗi waɗanda suka kai har N833k, ko da babu ko sisi a asusun ajiyar su, bayan bankin ya samu matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel