Aikatau: Jerin Jihohi 5 Mafi Muni a Arewacin Najeriya Ta Fuskar Bautar da Kananan Yara

Aikatau: Jerin Jihohi 5 Mafi Muni a Arewacin Najeriya Ta Fuskar Bautar da Kananan Yara

  • Kananan yara na ci gaba da shan wahalar aikatau a Najeriya, musamman ma a Arewacin kasar, kamar yadda rahoton hukumar NBS ya nuna
  • Hukumar kididdigar ta fitar da sabon rahoto da ya nuna jihohi 10 daga Arewa da Kudu da bautar kananan yara ya fi muni
  • Jihohin da aka fi samun rahoton tursasa kananan yara yin aikatau su ne Cross Rivers, Yobe, Abia da Filato, amma za mu fi karkata kan Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cewar wani rahoto da hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya nuna cewa akalla kananan yara miliyan 24 ake tursasawa yin aikin kudi a kasar.

A cikin su kuma akwai akalla yara miliyan 14.3 da ake aikin aikatau mai hatsarin gaske ga lafiya da rayukansu, rahoton jaridar Tribune Online.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Rahoton bautar kananan yara a jihohin Najeriya
Hukumar NBS ta fitar da rahoton jihohin Najeriya da aka fi bautar da kananan yara. Hoto: @NBS_Nigeria
Asali: Twitter

Kididdigar NBS ta kuma nuna cewar akalla kananan yara miliyan 14 ke aiki mai hatsari daga shekarar 2022 zuwa yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana bautar da miliyoyin yara a Arewa

Rahoton hukumar NBS ya nuna cewa jihohin Arewa masu Yamma sun fi yawan kananan yara da ke aikin bauta, wanda adadin su ya haura miliyan 9.

A cewar rahoton jaridar Premium Times, yara hudu cikin 10 a Najeriya na rayuwa a mawuyacin hali.

Haka zalika NBS ta ruwaito cewa kananan yara masu shekaru biyar zuwa 17 na yin aikatau na akalla awanni 14.6 a kowanne mako.

Jerin jihohin Arewa mafi muni a bautar da kananan yara:

1. Jihar Yobe

Jihar Yobe na da kaso 62.6% na ƙananan yaran da ake tursasawa yin aikatau a Najeriya. Ba iya kananan yara ba, hatta matasa na fuskantar wahalar aikatau a jihar.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Kamar yadda rahoton NBS ya nuna, ilimi, al'adu da kuma tattalin arziki sun taka rawa wajen jefa yara cikin ayyukan bauta a jihar Yobe.

2. Jihar Filato

Hukumar kididdiga ta NBS ta ce jihar Filato na da kaso 58.9% na kananan yara da suka fi shan wahalar yin aikatau a Najeriya.

Wannan adadin ya shafi yara 'yan kasa da shekara 18 yayinda a kuma abin ya fara watsuwa ga matasa da ke da kuruciya a tare da su.

3. Jihar Taraba

Jihar da Taraba ce ke bin bayan jihar Filato, wadda ke da kaso 58.6% a fannin tursasa kananan yara yin aikatau.

Jihar na da kananan yara 'yan shekara 12 zuwa 14 da ke aikin bauta yayin da bautar ta tsananta a yara masu shekara 14 zuwa 17.

4. Jihar Kogi

Akalla yara 'yan shekara 5 zuwa 17 suna aikatau a jihar Kogi, kuma adadin su ya kai kaso 54.4% na kididdigar NBS.

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Duk da cewa matasa da magidanta na fuskantar tasu bautar, sai dai jihar ta fi fama da matsalar bauta a tsakanin kananan yara.

5. Jihar Bauchi

Jihar Bauchi daga Arewa maso Gabas ce ke bin bayan Kogi, inda nan ma yara 'yan shekara 5 zuwa 11 ke shan wahalar aikatau din.

A yayin da take da kaso 53.3% na yaran da ake bautarwa, jihar na samun ci gaba ta fuskar aikin bauta ga yaran da ke tasowa.

Takaddamar tsofaffin gwamnoni da EFCC

A wani rahoton kuma, Legit Hausa ta tattaro maku jerin wasu tsofaffin gwamnonin Najeriya da suka nunawa hukumar EFCC jan ido a lokacin da aka je kama su.

Na baya bayan nan dai shi ne tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello wanda har yanzu yake wasan buya da jami'an hukumar da suka sha alwashin kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel