Budurwa ta danna wa tsohon saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000

Budurwa ta danna wa tsohon saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000

  • Dakarun yan sanda sun yi ram da wata matashiyar budurwa bisa zargin halaka tsohon saurayinta kan kudi a Legas
  • Matar wacce ta yi dana sanin abin da ta aikata, tace lamarin ya fara ne daga kyautar N3,000 da aka musu su raba
  • A cewarta ta yi amfani da wuka wajen yankarsa a wuya ne yayin da take kokarin kare kanta daga zaluncinsa

Lagos - Rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta damƙe wata budurwa yar shekara 26, Oluwatoyin Joshua, bisa zargin sheƙe tsohon saurayinta.

Tribune Online ta rahoto cewa ana zargin matashiyar ta sheke saurayin ne kan kyautar N3,000 a yankin Shangisa dake cikin Legas.

Jami'i mai zana hotuna na hukumar, Adekunle Ajisebutu, a madadin kwamishinan yan sanda, ya ce wani mai kyakkyawan niyya ne ya ba su kyautar kudin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tsagin Mala Buni ya kwace ikonsa a Hedkwatar APC, ya faɗi gaskiyar abun da ya faru

Yan sanda a Legas
Budurwa ta danna wa tsohon saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Budurwar, wacce ta shiga dana sani kan abin da ta aikata tace ta halaka tsohon saurayin nata ne a kokarin kare kanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinta ta ce:

"A ranar na je ganin tsohon saurayina Adebayo a wurin da yake siyar da muggan kwayoyi, ina wurin wani abokinsa, ɗan danfarar Intanet ya zo ya bani kyautar N3,000, lokacin ya na shirin yin tafiya."
"Ya umarci na ɗauki dubu ɗaya na bai wa tsohon saurayi na N2,000, daga nan ya yi tafiyarsa. Saboda haka naje wurin Adebayo domin na sanar masa yadda muka yi da abokinsa."
"Nan fa ya ce ƙarya nake yi baki ɗaya kuɗin nasa ne. Na faɗa masa bai isa ya kwace kuɗin duka ba, na aje masa N2,000 a kan Tebur na kama gabana."

Meya jawo har akai kisan?

A cewar matashiyar budurwan, nan take sai ya watsa mata kudin a fuska, ya ɗauki waya ya kira mutumin da ya ba su kudin.

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Ta cigaba da cewa:

"Kafin na ankara ya fara jibgata, na kai kararsa wurin dattijon Anguwa, ya gargaɗe shi ya kuma umarce shi ya bar wurin baki ɗaya."
"Bayan an fitar da shi da tsiya sai ya sake dawo wa ya cigaba da narka ta, garin haka ne na shiga ɗakin girki na sunkuto wuƙa domin na tsorata shi."
"Ina kokarin guduwa daga wurinsa ne ya sa wani fasasshen tayil ya dake ni a ka, ni kuma na yanke shi a wuya, nan da nan aka kai shi Asibiti, bayan awa uku ya ce ga garinku nan. Ni na biya kudin kai shi Asibiti."

A wani labarin kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon magidancin da ya gwangwaje matarsa da sabuwar mota a asibiti bayan ta haifa 'dansu na farko

Asali: Legit.ng

Online view pixel