Kisan Hanifa: Abin da ya sa Gwamnatin Kano ta ba Abdulmalik Tanko aron Lauya a kotu

Kisan Hanifa: Abin da ya sa Gwamnatin Kano ta ba Abdulmalik Tanko aron Lauya a kotu

  • Matashin lauyan nan mai kare hakkin Bayin Allah, Abba Hikima ya tabo shari’ar Hanifa Abubakar
  • Abba Hikima esq ya ce dokar kasa ta ce dole ne a tanadi Lauyan da zai tsayawa Abdulmalik Tanko
  • Muddin hukuncin zai iya zama mai girma, dokar kasa ba ta yarda mutum ya kare kan shi a kotu ba

Kano - Abba Hikima, wani Lauya mai kare hakkin al’umma a jihar Kano ya fitar da mutane daga duhu a game da lamarin shari’ar kisan Hanifa Abubakar.

Barista Abba Hikima ya yi karin haske ne bayan ya ji mutane da-dama sun fito su na korafi a dalilin ba Abdulmalik Tanko lauya da gwamnatin Kano ta yi.

A shafinsa na Facebook, Hikima ya ce akwai dalilin da ya sa aka ga an dauki wannan matakin.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

Abdulmalik Tanko shi ne wanda ake zargi ya kashe Hanifa Abubakar bayan ya yi garkuwa da ita. Wannan mutumi ya amsa laifinsa da yake hannun ‘yan sanda.

Labari zai canza?

Da aka shiga kotu, sai aka ji labari ya na neman canzawa, Tanko ya ce bai aikata laifi ba. Gwamnatin Kano kuma ta bukaci a ba shi hayar mai kare shi.

Barista Hikima ya ce a dokar Najeriya, dole ne gwamnati ta ba Abdulmalik Tanko aron lauya da zai kare shi idan ana shari’ar da za ta iya kai ga hukuncin kisa.

A cewar wannan lauya, ba zai yiwu a kyale malamin makarantar ya kare kan shi a kotu ba, tun da akwai yiwuwar zartar masa da hukunci mafi tsauri a doka.

Gidan Hanifa Abubukar
Mataimakin shugaban kasa a gidan Hanifa Abubukar Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Saboda haka ya zama dole a nemi hayar lauyan da zai kare Tanko a gaban Alkali, domin hakan ba ya nufin za a juya gaskiya, sai don kurum ayi wa kowa adalci.

Kara karanta wannan

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Kamar yadda Hikima ya rubuta a shafin na sa, kamata ya yi mutane su yi murna domin an fara cika sharudan da ake bukata domin doka ta yi aikinta a shari’a.

Abin da Lauya yake cewa

“Na ji har yanzu jama'a su na ta sukar gwamnatin Kano akan daukarwa Abdulmalik Tanko lauya, da kuma canza ikirarin da shi Abdulmalik yayi na cewa shine ya kashe Hanifa kamar yadda yayi a hannun jami'an tsaro.”
“To yana da kyau jama'a su sani cewa daukarwa Abdulmalik Tanko lauya wajibi ne a irin wannan sharia. Ba zai yiwu ayi wa mutum sharia akan laifin da za'a iya yanke wa mutum hukuncin kisa ba har sai idan mutun yana da lauya.”
“Saboda haka mu da muke fatan ganin anyi wa Hanifa da iyayen ta adalci, kamata yayi muyi farin ciki cewa an cika sharadin shari'ar- wato daukar wa Abdulmalik lauya.”
“Haka kuma a irin wannan shariah ko da shi Abdulmalik ya kuma amsa cewa shi ya kashe Hanifa a gaban alkali to dokokin gabatar da irin wannan kara ba su yarda alkali ya rubuta masa cewa ya amsa ko kuma yayi masa hukunci take yanke ba.”

Kara karanta wannan

Yadda manya suka yi kokarin wanke Abba Kyari daga badakaloli amma abin ya faskara

“Wajibi ne ko da mutum ya amsa laifinsa a gaban alkali, in dai hukuncin kisa yake fuskanta, to wajibi ne masu gabatar da kara su kawo hujjjojin su kuma a gabatar da shariar kamar yadda za'a yi wa wanda bai amsa ba.”
“Saboda haka wannan ma ba wata matsala bace. Saboda haka jama'a su kwantar da hankalin su inshaAllah gaskiya zata yi halin ta.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel