Bidiyon Bafullatanin da ya haddace duka kananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya

Bidiyon Bafullatanin da ya haddace duka kananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya

  • Bidiyon wani da ya san duka kananan hukumomin Najeriya yana yawo a shafukan sada zumunta
  • Wannan Bafullatani mazaunin Jigawa ya san adadin kananan hukumomin da ke kowace jihar kasar nan
  • Za a ji wannan ‘Dan baiwa yana jero wasu sunayen kananan hukumomin ba tare da ya yi mantuwa ba

Wani mutumi ya na yawo a kafofin sada zumunta na zamani saboda irin baiwar da Allah ya yi masa na karfin harda.

Kamar yadda za a iya gani a bidiyo, wannan Bafullatani ya san kowace karamar hukuma da ake da ita a duk fadin Najeriya.

Nura Sabitu ya wallafa bidiyon mutumin Jigawa da kawo yanzu ba a san sunansa ba, wanda ya san sunayen ko ina a kasar nan.

Babu wata karamar hukuma da wannan Bawan Allah bai hardace sunanta ba. Da wahala a samu wani wanda zai iya kure shi.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Za a ji ana tambayar wannan mutum a kan kananan hukumomin da ake da su a wasu jihohi, nan take zai jero su, ba sai ya duba ba.

Abuja
Birnin Tarayya Abuja Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baya ga sanin sunan kowace karamar hukuma a Najeriya, za a ji cewa ya kuma san adadin kananan hukumomin da ke kowace jiha.

Da aka tambaye shi game da kananan hukumomin da ke Abia, sai ya ce da jihar Abia, da Enugu, Filato, da kuma Yobe duk 17 ake da su.

Kafin a ce kobo, sai ya fara jero kananan hukumonin Abia tun daga Aba ta Arewa, zuwa Ohafiya har karshe ba tare da an tuna masa ba.

A game da Imo kuwa ya ce adadin kananan hukumominta 27 daya ne da Jigawar da yake zama da Borno a Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kone gine-gine 110 a Chibok, Zulum ya je ziyarar jaje

Haka zalika za a ji wannan Bafullatani ya jero duka kananan hukumomin da ke jihar Katsina tun daga su Baure har zuwa Zango.

A bidiyon za a ji ya fara jero kananan hukumomin da suke Kaduna ya ce jihar tayi tarayya da Ribas da Benuwai da Sokoto a adadinta.

A karshen bidiyon za a ji shi ya fara jero kananan hukumomin jihar Kaduna irinsu Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Ikara, Jabba da sauransu.

Garkuwa da mutane

Dazu aka ji labarin wata ‘yar kasuwa da ke zaune a garin Zaria, jihar Kaduna ta na shari’a da ‘danuwanta na jini a gaban Alkali a kotu.

Hajiya Binta Mohammed ta bada labarin yadda ‘danuwanta ya sa aka yi garkuwa da ita bayan ta nemi ya ba ta wasu kudinta da ke hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel