Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya hadu da masu yi masa fafutuka a zaben 2023
  • Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya sa labule da wadannan mutane a wani otel a jihar Bayelsa kwanaki
  • Akwai magoya bayan da suke sha’awar ganin Jonathan ya sake komawa kujerar shugaban kasa

Bayelsa - Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya gana da jagororin kudu maso kudu da suke sha’awar ganin ya koma kan mulki a 2023.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 3 ga watan Junairu, 2022 cewa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya yi wannan zama ne a jiharsa ta Bayelsa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana a ranar 27 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, tsohon shugaban kasar ya hadu da masu son ganin ya koma mulki.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

An yi taron ne a wani otel mai suna Aridolf Hotels and Spars a garin Yenagoa, jihar Bayelsa. Ana zargin Madam Patience Jonathan ce ta mallaki wannan otel.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa bayan wannan zama da aka yi ne aka ga Jonathan ya kai wa shugaban kasa Buhari ziyara a fadar shugaban Najeriya.

Goodluck Ebele Jonathan
Shugaban kasa Buhari da Goodluck Ebele Jonathan Hoto: @orbitnewsng
Asali: Facebook

Kokarin Dikivie Ikiogha da mutanensa

Cif Dikivie Ikiogha ne ya ke jagorantar tafiyar South-South Presidency 2023, ya na ta ganawa da masu ruwa da tsaki domin ganin Jonathan ya koma Aso Villa.

Ko da cewa a ‘yan kwanakin baya. wannan kungiya tayi shiru, ana sa ran cewa a wannan shekara za ta cigaba da fafutuka tun da zabe ya fara matsowa.

“Jagororin kungiyar da ke kitsa dawowar Jonathan fadar Aso Rock a 2023 sun yi hadu da Jonathan a otel din mai dakinsa, Aridolf Hotels and Spars.”

Kara karanta wannan

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

“Shugaban tafiyar, Cif Dikivie Ikiogha da wasu jagorori na yankin kudu maso kudu sun halarci taron. Jonathan ya tofawa yunkurin na su albarka.”
“Tsohon shugaban kasar ya fada masu su koma jihohinsu, su cigaba da wannan gwagwarmaya.” -Majiya.

Lissafin wasu manyan APC

Tun tuni aka ji cewa wasu kusoshin jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya su na kokarin ganin Jonathan ya bar PDP domin a ba shi tikitin APC na takara a zaben 2023.

Yin hakan zai taimaka mulki ya sake dawowa yankin Arewa a 2027 domin wa’adi daya ya ragewa Dr. Jonathan, don haka zai mika ragamar bayan shekaru hudu.

Ana zargin wani gwamna daga Arewa da ya dage a kan wannan batu ya na so ya zama mataimakin shugaban Najeriya idan suka fito takara tare da Jonathan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel