Tsohon masoyin shahararriyar ‘Yar fim ya karbe motarsa bayan an yi mummunar rabuwa a fili

Tsohon masoyin shahararriyar ‘Yar fim ya karbe motarsa bayan an yi mummunar rabuwa a fili

  • Tsohon saurayin Tonto Dikeh, Prince Kpokpogri ya karbe wata motarsa da ke hannun ‘yar wasar
  • A shafinsa na Instagram, Kpokpogri ya tabbatar da cewa wannan mota Lexus SUV ta dawo hannunsa
  • Hakan dai ya faru ne bayan ‘dan siyasar ya rabu da budurwar ta sa a wani irin kazamin yanayi kwanaki

Delta - Prince Kpokpogri wanda a da yake tare da tauraruwan ‘yar wasar kwaikwayo, Tonto Dikeh, ya karbe wata motarsa da ta dade a hannunta.

Legit.ng ta samu labari cewa bayan wata da watanni ana ta rigima kan abu daya, Prince Kpokpogri ya yi nasarar karbe wannan mota Lexus SUV.

Idan za a iya tunawa, a baya Kpokpogri mai shekara 37 ya zargi Tonto Dikeh da rike mabudin motarsa, duk da kowa ya kama hanyar gabansa a yanzu.

Kara karanta wannan

Uwar 'Yan Crypto: Matar da ta ajiye aiki, ta rungumi Crypto, ta koma samun N30m a wata

Bayan ‘dan siyasar na Delta ya rabu da Dikeh wanda ta shahara a Nollywood, kowanensu ya zo dandalin sada zumunta, ya na maganganu marasa dadi.

Tsohon masoyin shaharriyar ‘Yar fim ya karbe motarsa bayan an yi mummunar rabuwa a fili
Prince Kpokpogri a motarsa Hoto: @kpokpogri, @tontolet
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kpokpogri ya tabbatar da karbe motarsa

A wani gajeren bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, an fahimci cewa wannan mutumi ya samu ya karbi mabudin motarsa, har ya tuka abinsa.

Za a ga Kpokpogri ya na murmushi, ya na gaida mabiyansa a wannan bidiyo da yake yawo.

Da wata Baiwar Allah tayi masa magana, ta na taya shi murna, Kpokpogri ya tabbatar da cewa ya karbe wannan motar mai tsada a hannun Dikeh.

Tsohon masoyin shaharriyar ‘Yar fim ya karbe motarsa bayan an yi mummunar rabuwa a fili
Prince Kpokpogri ya karbe motarsa Hoto: @kpokpogri / Instagram
Asali: Instagram

Martanin masoya a shafukan zumunta

Tuni mabiya da masoya su ka fara tofa albarkacin bakinsu a game da wannan lamari bayan ganin bidiyon ya karade dandalin sada zumuntan.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamna ya sallami hadiminsa kan rubutun rashin kunya Facebook

“Mutum ya karbe kayansa ma abin murna ne, ba kowa zai iya ba.”

- Cjazter

"Na tabbata Poko ta karbe na ta kayan kafin ta bada motar nan."

- Uddiegirl:

"Ita ma Tonto ta karbi motarta Hilux. An yi daidai kenan. Kuma za ma ta iya sayen biyar na irin wannan Lexus."

- Mariam_adun

Mutuwar aure da ake samu

A shekarar nan, igiyar aure da yawa sun tsinke, daga cikin wadanda abin ya shafa har da fitattun attajirai da shaharrun taurarin da ake ji da su a Duniya.

A 2021 aka ji cewa babu aure tsakanin Sani Danja da Mansurah Isah. Haka zalika Bill Gates da Melinda Gates da suke tare tun 1987 sun rabu kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel