Bill Gates, Kanye West, Sani Danja da shahararrun mutanen da aurensu ya mutu a 2021

Bill Gates, Kanye West, Sani Danja da shahararrun mutanen da aurensu ya mutu a 2021

  • A shekarar nan, igiyar aure da yawa sun tsinke, daga cikin wadanda abin ya shafa har da fitattu
  • Bill da Melinda Gates da suke tare tun 1987 sun ba kowa mamaki da suka sanar da mutuwar aurensu
  • A wannan shekarar ne aka samu labarin cewa babu aure tsakanin Sani Danja da Mansurah Isah

Duk da cewa miliyoyin mutane sun yi aure a shekarar nan ta 2021, sai dai kuma an ji labarin mace-macen aure da yawa da suka ba mutane mamaki.

Jaridar Punch ta tattaro jerin wasu aure da suka mutu a shekarar bana. Ga wasu nan daga cikinsu:

1. Bill da Melinda Gates

Wani labarin mutuwar aure da ya girgiza Duniya a 2021 shi ne na Bill Gates da mai dakinsa Melinda. Kafin rabuwarsu, sun yi kusan shekara 30 tare.

Kara karanta wannan

Manyan ayyuka 5 da wasu gwamnonin Najeriya suka aiwatar a 2021

2. Elon Musk da Grimes

A watan Satumban bana rahotanni suka bayyana cewa Elon Musk ya sake rabuwa da sahibarsa Grimes. Babban Attajirin ya saba rabuwa da matan aurensa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Kim Kardashian da Kanye West

A karshen shekarar nan Naomi Silekunola mai shekara 28 ta bada sanarwar cewa ta bar gidan mijinta, Mai martaba Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II.

Mutanen da aurensu ya mutu a 2021
Bill Gates, Ooni, Musk, Kim, da Danja
Asali: UGC

4. Laurent da Simone Gbagbo

A watan Yunin bana aka ji cewa tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo zai saki matarsa, Simone wanda sun yi sama da shekaru 30 da yin aure.

5. Paul da Anita Okoye

Wasu fitattun mutanen da suka rabu a shekarar nan su ne Anita da Paul Okoye. Daya daga cikin mawakan na PSquare ya rabu da uwar ‘ya ‘yansu da ya aura a 2014.

6. Oonin Ife da Naomi Silekunola

Kara karanta wannan

Manyan tirka-tirka da abubuwan mamaki da aka gani a Majalisar Tarayya a shekarar 2022

A karshen shekarar nan Naomi Silekunola mai shekara 28 ta bada sanarwar cewa ta bar gidan mijinta, Mai martaba Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II.

7. Sani Danja da Mansurah Isah

An kuma samu labari maras dadi cewa Mansurah Isah ta koma gidan haya bayan tsinkewar igiyar auren ta da fitaccen ‘dan wasan fim, Sani Musa Danja.

Rahoton yace sauran sarakunan da aurensu ya mutu sun hada da Oluwo na Iwo, Mai martaba Oba Abdulrosheed Akanbi mai auren wata mata ‘yar kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel