Uwar 'Yan Crypto: Matar da ta ajiye aiki, ta rungumi Crypto, ta koma samun N30m a wata

Uwar 'Yan Crypto: Matar da ta ajiye aiki, ta rungumi Crypto, ta koma samun N30m a wata

  • Brenda Gentry wata mata ce wanda ta yi murabus daga wurin aiki, ta kama harkar ‘Cryptocurrency’
  • Yanzu ana yi wa wannnan Baiwar Allah lakabi da ‘Crypto Mum’ a kasar Amurka saboda irin gawurtar da ta yi
  • A kowane wata, Brenda Gentry ta na iya tashi da dala $80, 000, wanda ya zarce albashinta na shekara daya a da

Akwai ganganci a ce mutum ya ajiye aikin da ake biyansa albashi, ya rungumi wani abin da bai da tabbas, wannan shi ne labarin Brenda Gentry.

A watan Oktoban 2021, Brenda Gentry ta ajiye aikinta a wani kamfani a kasar Amurka, tun daga nan ta tsunduma cikin harkar canji da cinikin Crypto.

CNBC tace Misis Brenda Gentry mai shekara 46 tayi dace, domin kwalliya ta biya mata kudin sabulu. Yanzu ta na samun makudan kudi duk wata.

Kara karanta wannan

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

Wannan mazauniyar ta garin San Antonio, kasar Amurka ta shaidawa gidan talabijin na CNBC cewa yanzu ta na tashi da kusan dala $80, 000 a wata.

Rahoton da muka samu shi ne, Gentry ta ajiye aikinta ne a lokacin da ake tsakiyar annobar COVID-19, ta saye kudin yanar gizo na Cryptocurrency.

Uwar 'Yan Crypto
Brenda Gentry da 'Ya 'yanta Cynthia Imani Gentry Hoto: www.cnbc.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abu kamar wasa ... harka ta mike

Da yake ta na da ilmin tattalin arziki, ta fara sannu a hankali, har ya kai ta saye hannu da yawa. Zuwa 2021, Gentry ta fara ganin ribar abin da ta saya.

A wata shida darajar abin da ta mallaka ya tashi sosai a kasuwa, daga nan abubuwa suka fara kyau ga wannan Baiwar Allah da ake kira ‘Crypto Mum’

Yanzu ta yi kudi a wannan harka ta Crypto, ta na kuma cigaba da kasuwancin da kamfaninta na Gentry Media Productions da kuma wasu ‘ya ‘yan ta biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

Nawa Brenda Gentry ta ke samu?

Kamfanin na ta yana samun tsakanin fam $40,000 zuwa $80,000 a wata. Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, ta kan iya samun Naira miliyan 33 a wata.

A lokacin da ta ke aikin kamfani kuwa, albashinta a shekara bai wuce $75,000 ba. Hakan ya na nufin za ta iya samun albashinta na shekara a kwana 30.

Mutumin Najeriya zai je kurkuku

Dazu kun ji cewa wata Kotu ta samu wani mutumin garin Middletown da laifin kwanciya da marasa lafiya a kasar Amurka, an daure shi ne shekaru uku.

Wannan mutumi mai suna Godbless Uwadiegwu, ma’aikacin wani asibiti ne a yankin Warren County, kasar Amurka, da yake kwanciya da marasa lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel