Har Yanzu Ina Son Fatima, Ba Zan Fasa Auren Ta Ba, In Ji Saurayi Habib Suleiman Da Budurwarsa Ta Daɓa Wa Wuƙa

Har Yanzu Ina Son Fatima, Ba Zan Fasa Auren Ta Ba, In Ji Saurayi Habib Suleiman Da Budurwarsa Ta Daɓa Wa Wuƙa

  • Habib Suleiman, mazaunin Unguwan Rogo da ke Jos ta arewa a jihar Filato ya ce yana nan a kan bakarsa na auren budurwarsa
  • Duk da budurwa tasa, Fatima Danjuma ta sharba masa wuka sakamakon wani rikici da ya shiga tsakaninsu, ya ce hakan bai canja komai ba
  • A cewarsa, fushi ya janyo hakan sakamakon kishin da ya tunzurata bayan ganinsa tare da wata budurwar, hakan ya sa ta yi aika-aikar amma ya yafe mata don har hakuri ta ba shi

Jihar Filato - Habib Suleiman, mazaunin Unguwan Rogo da ke karamar hukumar Jos ta arewa ya ce bai sauya ra’ayinsa ba akan auren budurwarsa, Fatima Danjuma, duk da ta datse shi da wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A raba mu, duka take lakaɗa min har da damƙar mazakuta na, Magidanci ya yi ƙarar matarsa Fatima

Fatima ta na zama ne a Ali Kazaure da ke karkashin karamar hukumar Jos ta arewa, kuma ‘yan sanda sun yi ram da ita a ranar 2 ga watan Disamba bayan an zargeta da datsar saurayinta da wuka bayan wani rikici ya shiga tsakaninsu.

Har Yanzu Ina Son Fatima, Ba Zan Fasa Auren Ta Ba, In Ji Saurayi Habib Suleiman Da Budurwarsa Ta Daɓa Wa Wuƙa
Saurayin da budurwarsa ta daba wa wuka ya ce ba zai fasa auren ta ba. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Duk da dai ta musanta zargin da ‘yan sanda su ka yi mata na sharba wa Habib wuka, amma bincike ya nuna cewa ita ce ta yi aika-aikan bayan wani rikici ya shiga tsakaninsu.

Kishi ne ya tunzura ta

A cewar Habib, Fatima ce ta datse shi da wukar bayan ta gan shi tare da wata budurwa su na tafiya, daga nan ta zargi cewa budurwarsa ce.

Daily Trust ta gano yadda ya bayyana cewa yarinyar kanwar abokinsa ce, inda ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

“Bayan ta zo wucewa tare da kawarta ta gan ni da wata mun jero, na lura ta fusata saboda na yi kokarin kiran sunanta amma ta ki amsawa saboda tsabar kishi.
“Ban san cewa bayan ta ganni ba ne ta tsaya makwabta ta amshi wuka. Kamar daga sama na ji ta sharba min wukar wanda daga nan aka wuce da ni asibiti.
“Amma duk da haka ina son Fatima. Kuma ina nan da niyyar aurenta. Abinda ya faru tsakaninmu kaddara ce wacce za ta iya afka wa kowa. Muna son junanmu, fushi ne ya janyo ta yi aika-aikar.”

Ya ce ta ba shi hukuri kuma suna son junansu

Ya bayyana yadda har hakuri ta ba shi kuma ya yafe mata. Ya ce ya na neman taimakon mutane akan su taya shi rokon iyayensa don su amince ya aureta.

Don nuna mata cewa yana tare da ita, ana sallamarsa daga asibiti ya biya wurinta a ofishin ‘yan sanda inda ya nuna mata tausayi.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa

Mahaifiyarsa ta ce sai ta raba su

Yayin da aka tuntubi mahaifiyar Habib, Maryam Suleiman, ta yi mamakin yadda aka yi yarinyar da ya ke so ya aura har ta iya datsarsa da wuka.

Ta mika godiyarta ga Ubangijin da ya raya shi, kuma ta ce a baya su na shirye-shiryen biyan sadakinta amma yanzu sun sauya ra’ayi.

A cewarta, sai ta dakatar da soyayyar saboda ta na tsoron za ta iya kashe shi idan sun yi aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel