Jafar Jafar: Bayan wata 5, Ganduje ya biya ‘dan jaridar da ya bankado ‘faifan dala’ N800, 000

Jafar Jafar: Bayan wata 5, Ganduje ya biya ‘dan jaridar da ya bankado ‘faifan dala’ N800, 000

  • Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bi umarnin kotu a shari’arsa da Jafar Jafar
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya biya ‘dan jaridar N800, 000 kamar yadda Alkali ya umarce shi
  • Jafar Jafar wanda ba ya Najeriya a halin yanzu, ya tabbatar da cewa kudin sun shigo hannunsa

Kano - Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya biya kudin da kotu ta bukata ga Jafar Jafar, kamar yadda Alkali ya umarce shi.

Shugaban gidan jaridar na Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya nuna cewa wadannan kudi sun shigo hannunsa a wani bayani da ya yi a shafinsa na Facebook.

‘Dan jaridar ya kyankyasa wannan ne a safiyar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, 2021. Sai dai Jafar bai fito ya bayyana adadin abin da gwamnan ya aiko ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu

Malam Jaafar Jaafar ya rubuta cewa: “Alert ya shigo. Ku tafa wa na Gwaggo.”

Bayan haka, ‘dan jaridar ya shaidawa gidan rediyon Freedom na garin Kano cewa an biya shi kudin kamar yadda Alkali ya bada umarni a watan Yuli.

Jafar Jafar
Jafar Jafar da Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Jaafar.Jaafar/The Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da mutane suke fada a Facebook

Yayin da aka aikawa Jafar wadannan kudi har N800, 000 a asusunsa, mutane sun fito su na ta tofa albarkacin bakunansu a dandalin sada zumuntan a yau.

DAMA RASHIN HAKURINKA NE AI – Murtala Tahir
Ina sauraron kasona oger tun da dai all 2gether - Ibrahim Tanko
Wallahi in nine ganduje bazan bada ba – Sulaiman Danlami Mekwano
Anyo canjin dollar's kenan? – Abdulazeez Abbas
Na gwaggo yashiga taitayinsa kenan – Haruna Abdullahi
Tab, kace dai kaima ya dan tsakura ma kenan. *Dariya* – Kamilu Garba Fagge

Kara karanta wannan

Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

Shari'ar Jafar Jafar da Gwamna

Idan za ku tuna, tun a watan Yuli Jafar Jafar yake sauraron wadannan kudi bayan babban kotun jihar Kano da ke Bompai ta zartar da hukunci a kan gwamna.

Gwamnan Kano ya kai fitaccen ɗan jaridar wanda ya rika wallafan bidiyoyin zargin zuwa kotu, da sunan an bata masa suna, amma daga baya ya janye tuhumarsa.

Alkali mai shari’a Suleiman Danmalam ya bukaci Gwamna Ganduje ya biya Jaafar da gidan jaridarsa, N800, 000 a dalilin bata masa lokaci da aka yi a shari'ar.

Tun a watan Mayu dai Jafar ya tsere daga Najeriya, ya tafi Ingila ya tare da cewar rayuwarsa na fuskantar barazana, yace ba zai dawo gida ba sai ya samu amince.

Asali: Legit.ng

Online view pixel