Jafar Jafar zai bada sadakar duk tarar N800, 000 da Gwamnan Kano Ganduje ya biya shi

Jafar Jafar zai bada sadakar duk tarar N800, 000 da Gwamnan Kano Ganduje ya biya shi

  • Malam Jafar Jafar ya bayyana abin da zai yi da tarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya biya shi
  • ‘Dan jaridar yace zai bada wannan kudi a gidan rediyo domin a taimakawa masu karamin karfi
  • Baya ga kudin tarar na N800, 000, Jafar Jafar ya yi alkawarin zai kara da N200, 000 su cika miliyan

United Kingdom - Fitaccen ‘dan jarida, Jafar Jafar, ya bada sanarwar cewa zai bada sadakar kudin da gwamnan jihar Kano ya ba shi a shari'ar faifen Dala.

Jaafar Jaafar mai jaridar nan ta Daily Nigerian ya bayyana abin da zai yi da kudin da Abdullahi Umar Ganduje ya biya shi a dalilin bata masa lokaci a kotu.

Daily Nigerian Hausa ta rahoto Jafar Jafar ya na bayanin inda zai saka wadannan makudan kudi.

Read also

Da dumi-dumi: Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar

Da aka yi hira da ‘dan jaridar a gidan rediyon Freedom na jihar Kano, ya shaida cewa zai bada sadakar kudin ne ga shirin nan na ‘Inda ran ka’ da ake yi.

A wannan shiri da ya yi suna a gidan rediyon, akwai wani bangare da aka ware na musamman inda mutane ke kawo kokon barar kudin asibiti da makaranta.

Gwamnan Kano Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje Hoto: dailypost.ng
Source: UGC

Jafar Jafar zai kara da N200, 000

Jafar ya fadawa ‘yan jaridar wannan ne da suka yi hira da shi a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba, 2021, ya yi alkawarin zai hada da shi gudumuwar.

Malam Jafar yace zai kara N200, 000 a kan wannan kudi ta yadda za su kai miliyan daya, N1, 000, 000.

A halin yanzu da ake ta wannan tirka-tirka, Malm Jafar Jafar ba ya Najeriya, yana kasar Ingila tun bayan da ya yi kukan cewa rayuwarza na fuskantar barazana.

Read also

Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan kudin Janar Abacha da aka dawo da su a 2020

Malam Jafar ya sulale daga garin Abuja ne bayan ya bankado wasu faya-faye da suke zargin gwamna Abdullahi Ganduje daga karbar rashawar kwangiloli.

Jafar Jafar ya karbi N800, 000

A karshen makon jiya ne ku ka ji cewa an biya Jafar Jafar N0.8m bayan bata masa lokaci da gwamnan jihar Kano ka yi a gaban kotu a shari'ar da suke yi.

Mutane su na ta magana yayin da Gwamna ya biya ‘dan jaridar wadannan kudi bayan ya shaidawa Duniya cewa kudin sun shigo asusun bankin na sa.

Source: Legit.ng

Online view pixel