Latest
Jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Alhaji Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya bayyana nadamarsa kan zabar Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2023.
Babbar jam'iyyar adawa na ci gaba da raba gari da manyan kusoshinta da tsohon muƙaddashin shugaban PDP a Ebonyi ya tattara magoya bayansa suka koma APC.
Rahoto ya zo cewa kusa a jam'iyyar APC, kuma tsohon kwamishina, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce yan adawa sun kullo makircin bata wa shugaban hukumar NAHCON suna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fitaccen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta da ta sa ya fara yin haushin kare.
Dubun wani baragurbin likita mai kula da lafiyar 'yan ta'adda ta cika a jihar Katsina. Likitan ya amsa zargin da ake masa inda ya yi bayani kan ayyukansa.
An samu matsala a tushen wuta naƙasa, wanda ya janyo daukewar wuta a yankunan Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa. Ana kan aikin gyara tare da hukumomi.
Yawaitar hare-haren ƴan bindiga ya fusata mazauna Ungwan Ate a kaɗamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, sun fantsama kan tituna su na zanga zanga.
Shaidan jam'iyyar APC a kotun sauraron karar zaben Edo ya ce an yi tafka magudi a zaben. Ya ce an samu karin kuri'u sama da adadin wadanda suka yi rajista.
Yayin da ake tuhumar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta NHIS, Babbar kotun Abuja ta ki amincewa da ba da belin Farfesa Usman Yusuf kan badakalar kudi.
Masu zafi
Samu kari