Latest
Wasu barayi sun tafka sata ana tsaka da sallar tarawihi a wani masallaci a birnin tarayya Abuja ana tsaka da sallar tarawi. Ana neman barayin ido rufe.
Sanata Abdulaziz Yari ya kaddamar da raba kayan abinci har tirela 496 domin rabawa al'umma a dukkan kananan hukumomin jihar saboda fara azumin watan Ramadan.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa kotun koli ta tsige shi daga kujerar gwamna. Fubara ya ce yana nan daram.
Wani kusa a jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano ya fara shirin ganin ya sulhunta manyan jagororin siyasar Ƙano. Ya bayyana cewa hakan zai taimaki jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta zuba idanu wasu tsirarun 'yan siyasa suna kokarin jefa rayuwar jama'a a masifa ba.
Matatar Dangote ta dauki nauyin rage asara ga 'yan kasuwa da suka saye fetur a tsohon farashi domin su rage kudin mai a Najeriya. Dangote zai kashe N16bn kan haka
Majalisar dattawan kasar nan ta bayyana cewa ba ta da aniyar daukar mataki a kan zarin da ake yi wa shugabanta, Sanata Godswill Akpabio bisa zargin neman Natasha.
Gwamnatin jihar Borno, karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta sanar da dakatar da 'yan kasuwa daga biyan kudin haraji har na shekara biyu.
Kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da karin kudin wuta da gwamnatin Najeriya ke shirin yi. NLC za ta rufe Najeriya kirif da yin zazzafar zanga zanga ga Bola Tinubu.
Masu zafi
Samu kari