Latest
Kotun koli ta kasar Amurka ta soke umarnin Shugaba Donald Trump da ke ƙoƙarin takaita bai wa jariran da aka haifa a ƙasar zama 'yan ƙasa kai tsaye.
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa an kama wata mata, Sadiya Lwal bisa zargin yunkurin kashe mijinta da wuka yana cikin barci a gida.
Wani masoyin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya buƙaci a ƙara wa shugabannin Hukumar Kwastam ta Najeriya wa'adin aiki domin kawo ci gaba.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya mika bukatarsa ga hukumar INEC. Peter Obi ya bukaci a bayyana takardun karatun 'yan takara.
Dalibai 35 sun bace bayan harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar sakandare a Lassa jihar Borno, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da aikin ceto.
Hukumar jami'ar UNIOSUN ta bayyana cewa sojojin sun jikkata dalibai, sun kaace wayoyi da kwamfutoci a samamen da suka kai cikin daren Jjiya Litinin.
Wani saƙo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa an kama sarakunan Alabe da Babanla da matansu a Kwara bisa zargin garkuwa da mutane.
Daliban FUT Minna sun gudanar da zanga-zanga tare da toshe kofar jami’a saboda zargin yawaitar hare-haren fashi da rashin tsaro a wajen makaranta.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya mika sunayen kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar. Ya bukaci a tantance su don amincewa da su.
Masu zafi
Samu kari