Latest
Za ku ji wasu manyan dalilan da suka taimakawa Hon. Tajudden Abbas PhD wajen zama sabon shugaban majalisar wakilan kasar nan a zaben da aka gudanar yau a Abuja.
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zaɓi Bilyaminu Moriki a matsayin saɓon kakakinta. Hon. Bilyaminu ya samu hawa kan kujerar shugabancin ba tare da hamayya ba.
Moses Sule, sabon mamba a majalisar dokokin jihar Filato ya yi nasarar zama shugaban majalisa ta 10 yayin bikin rantsuwar kama aiki ranar Talata, 13 ga wata.
Sanata Barau Jibrin ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa a zaɓen da aka gudanar ranar 13 ga watan Yuni. Gogaggen ɗan siyasan ya fito daga jihar Kano.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar, CBN, Godwin Emefiele bisa zargin badakala da kuma daukar nauyin ta'addanci a kasar.
Dan majalisar wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Afam Ogene ya bayyana cewa a zuciyarsa Idris Wase yake so, amma wajen zaɓe, Abbas Tajuddeen ya zaɓa a zaɓen.
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ɗauki hutun kwanaki 21 domin tafiya ƙasar waje neman lafiya, ya miƙa mulki ga mataimakinsa kafin ya dawo a 6 ga Yuli.
Yan Najeriya za su so jin labarin wadanda za su shugabanci majalisa. Hon. Tajuddeen Abbas ya samu sauki a majalisar wakilai, amma an rasa gane zabin Sanatocin.
Rahotanni sun tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a wani ƙauye cikin jihar Kwara. Jirgin mai ɗauke da mutum 100 ya kife ne ana cikin tafiya.
Masu zafi
Samu kari