Latest
Tun bayan kona Qur'ani mai girma a Sweden, kasashe da mutane dai-daiku ke Allah wadai da aika-aika da aka yi a kasar, inda wasu ke kiran daukar matakai a gaba.
A Osun yaron Marigayi Isiaka Adeleke ya na cikin wadanda Gwamna ya ba mukami bayan shi kan shi. Akwai surukar Gwamnan da ta shiga Kwamishinonin da aka nada.
Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), ta ce babban abinda ya janyo tashin gwauron zabi da man fetur ya yi shi ne tsadar dalar Amurka. Kungiyar ta.
Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadin Kai' sun ragargaji ƴan ta'adda a jihar Borno. Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda shida tare da ƙwato makamai.
Shugaban gwamnonin APC (PDF) kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa shugaban jam'iyya da sakatare sun yanke yin murabus ne bisa ra'ayin kansu.
Tun bayan murabus na Sanata Abdullahi Adamu, jam'iyyar APC ke faman neman wanda zai maye gurbinsa, Tsohon gwamna Ganduje da Almakura na cikin masu neman kujerar
Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia, yace gwamnatinsa ta gano ma'aikatan bogi 2,500 kuma ta gano yadda ake tafka almundahana a tsarik biyan albashin ma'aikata.
Jigo a jam'iyyar APC mai mulki na ganin cewa bai wa tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje shugabancin jam'iyyar na iya kawo hargitsin da kan.
Masu goyon bayan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kan cire tallafin man fetur, sun gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya da ke a birnin tarayya Abuja.
Masu zafi
Samu kari