Zaben Kogi: Dan Takarar Sanatan SDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC Mai Mulki

Zaben Kogi: Dan Takarar Sanatan SDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC Mai Mulki

  • Ɗan takarar sanata a inuwar SDP a babban zaben 2023, Abdulrahman Tanko Ozi, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar Kogi
  • Jigon siyasar ya ayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna a inuwar APC mai mulki, Ahmed Ododo
  • Ya ce ya shiga APC tare da ɗumbin magoya bayansa bayan gano cewa Ododo ne ya dace da mulkin jihar Kogi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kogi state - Ɗan takarar sanatan Kogi ta yamma karƙashin inuwar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2023 da ya gabata, Dakta Abdulrahman Tanko Ozi ya sauya sheƙa zuwa APC.

Tsohon jigon SDP ya ce ya rushe baki ɗaya tsarin siyasarsa zuwa cikin jam'iyyar APC kuma ya sauya sheƙa tare da kafatanin magoya bayansa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ozi tareda ɗan takarar gwamnan APC a Kogi, Ododo.
Zaben Kogi: Dan Takarar Sanatan SDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC Mai Mulki Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mista Tanko Ozi ya ƙara da cewa ya umarci magoya bayansa su mara wa ɗan takarar APC, Ahmed Ododo baya a zaɓen gwamnan Kogi da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

Tsohon ɗan takarar Sanatan SDP ne da kansa ya bayyana haka a Lokoja ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023 lokacin da ya kai wa ɗan takarar gwamna a inuwar APC ziyara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa jigon siyasan ya zabi shiga APC da goyon bayan Ododo?

Tanko Ozi ya bayyana cewa ya yanke hukuncin mara wa Ododo baya ne bayan dogon nazari da gano cewa ba bu wanda ya cancanta da jan ragamar jihar Kogi kamar ɗan takarar APC.

A cewarsa, Mista Ododo zai ɗora daga inda gwamna Yahaya Bello zai aje bayan wa'adinsa ya ƙare.

Zamu ɗora kan nasarorin Yahaya Bello - Ododo

A nasa jawabin, ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Mista Ododo, ya yi maraba da Tanko Ozi zuwa cikin jam'iyyar APC kuma ya yi alkawarin ɗora wa daga kan inda Yahaya Bello ya tsaya.

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

Ya ce tsohon ɗan takarar sanatan ya ɗauki matakin da ya dace na sauya sheƙa daga jam'iyyar SDP domin bunƙasa jihar Kogi, rahoton Independent ya tabbatar.

Tanko Ozi ya riƙe kujerar shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Kogi a tsakanin 2007 zuwa 2011 lokacin yana matsayin mamba mai wakiltar mazabar Kogi Koton Karfe.

Babban Basarake, Chief Esogban Na Benin Ya Kwanta Dama Yana da Shekaru 93

A wani labarin na daban kuma Wani babban basaraken Benin a jihar Edo, Chief David Edebiri, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 93 a duniya.

Chief Esogban ya mutu ne ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023 a wani asibitin kuɗi da ke Benin, babban birnin jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel