Latest
Yayin da Kungiyar Kwadago ta NLC ke takun-saka da gwamnatin Najeriya, mun kawo muku rahoton kasashen Afirka da suka fi biyan mafi karancin albashin ma'aikata.
Wani kudirin doka da ke neman kafa wata jiha a shiyyar Kudu maso Gabas ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar wakilai. Za a rika kiran ta da 'Jihar Orlu'.
Rahotanni sun nuna cewa kwamitin mafi ƙarancin albashi ya koma teburin ci gaba da tattaumawa kan sabon albashin ma'aikata, ana tsammanin yau ne zaman ƙarshe.
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da fara gina titin karkara mai nisan kilomita 7.2 daga Mil Goma zuwa 'Yankatsari, da kilo mita 7.5 a Rijiyar Gwangwan kan N2.6bn.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya ce ba wani abun damuwa game da sabon mafi karancin albashi, ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsaurara matakan tsaro bayan an yawaita kai hari gidajen gyaran hali da guduwar fursunoni.
Yadda wasu direbobin kasar nan ke awon gaba da wasu jami'an tsaro idan an tsare su a hanya ya fara ci wa rundunar 'yan sandan kasar nan tuwo a kwarya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi manyan alkawura a lokacin da yake yakin neman zabe a shekarar 2023 amma bayan hawa mulki da shekara ya gaza cikasu.
Tun bayan zargin cewa mutuwar mawaƙi Mohbad ba ta Allah ba ce, gwamnati ta dora alhakin binciko dalilin mutuwar a wuyan asibitin koyarwa na jihar Lagos, (LASUTH).
Masu zafi
Samu kari