"A Sakar Mana Mara," NULGE ta yi Zanga Zangar Neman 'Yanci Daga Hannun Gwamnoni
- Kungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi (NULGE) ta goyi bayan gwamnatin tarayya wajen neman gwamnatocin jihohi su ƙyale ƙananan hukumomi su sarrafa kuɗinsu
- Shugaban NULGE a Yobe, Kwamred Umar Inusa ne ya jaddada goyon bayan yayin zanga-zangar neman ƴancin gashin kai daga gwamnoni da har yanzu su ka ƙi amincewa
- Wannan na zuwa a daidai gaɓar da gwamnatin tarayya ta maka gwamnonin Najeriya gaban kotu domin ganin an bawa ƙananan hukumomi damar sarrafa kuɗin su daga tarayya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe - Yayin da gwamnatin tarayya ta ja daga da gwamnatocin jihohi kan ba ƙananan hukumomi 'yancin gashin kai, kungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi a jihar Yobe sun yi zanga-zanga kan batun. A ranar Juma'a ne ma'aikatan a inuwar kungiyarsu ta NULGE suka yi zanga-zanga a karamar hukumar Nangere da ke jihar Yobe.
Leadership News ta wallafa cewa ma'aikatan sun ce lokaci ya yi da gwamnatin jiha za ta rabu da kananan hukumomi su ci gashin kansu.
'Dalilin yin zanga-zanga,' NULGE
A zantawarsa da manema labarai, shugaban NULGE a jihar, Kwamred Umar Inusa ya shaidawa manema labarai cewa dole ce ta sa su ka yi zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sun lura zanga-zanga ce kaɗai matakin da gwamnati ke fahimta, kuma lokaci ya yi da ya kamata a bar ƙananan hukumomi su yi amfani da kudin su da ake warewa daga gwamnatin tarayya.
Kwamred Umar Inusa ya jaddada cewa matukar aka bari ƙananan hukumomi su na sarrafa kuɗaɗensu, za a samu ci gaba da bunƙasar harkokin noma.
A baya Premium Times ta wallafa yadda gwamnatin tarayya ke goyon bayan ba wa ƙananan hukumomin ƴancin sarrafa kuɗaɗensu.
Gwamnati ta fadi dalilin kai gwamnoni kotu
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta fadi dalilanta na danganawa da kotu kan batun ƴancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce kamata ya yi gwamnoni su fifita buƙatar al'umma a kan tasu domin daga ƙananan hukumomi mafi akasarin masu zaɓe ke fitowa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng