Kwararrun Likitoci Sun Tono Dalilin Mutuwar Mawaƙi Mohbad Bayan Birne Shi

Kwararrun Likitoci Sun Tono Dalilin Mutuwar Mawaƙi Mohbad Bayan Birne Shi

  • Kwararrun likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar Legas (LUTH) sun gudanar da bincike kan gawar mawaƙi Ilerioluwa Oladimeji da aka fi sani da Mohbad
  • Bayanan binciken ya bayyana cewa an tono gawar mawaƙi Mohbad kwanaki takwas bayan binne shi tare da ɗaukar samfurin jini da bargo da wasu abubuwa
  • Da farko dai 'yan sanda sun zargi abokin marigayin mawakin Ibrahim Owudunni da aka fi sani da Primeboy da hannu wajen mutuwar Mohbad bayan sun yi faɗa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Lagos- Tun bayan zargin cewa mutuwar mawaƙi Ilerioluwa Oladimeji da aka fi sani da Mohbad ba ta Allah ba ce, gwamnati ta dora alhakin binciko dalilin mutuwar a wuyan asibitin koyarwa na jihar Lagos, (LASUTH). Bayan kammala bincike, bayanai sun ɓulla a kan abin da ake zaton shi ne ya yi ajalin mawaƙin.

Kara karanta wannan

Ruwa yayi gyara: Mamakon ruwa da iska ya lalata gidaje 100, an rasa muhalli a Plateau

Mohbad
Bincike ya bayyana yiwuwar wani ƙwaya da jikin marigayi mawaƙi Mohbad ne ya yi ajalinsa Hoto: Steven Chukwu
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa wani labari da ta kebanta da shi cewa an haƙo gawar Mohbad kwanaki takwas bayan an binne shi domin guda binciken.

Abubuwan da binciken gawar Mohbad ya gano

Bayan tono gawar marigayin aka dauko samfurin jininsa da samfurin abin da ke cikin ƙodarsa, ɓargo da hanta domin gudanar da binciken ƙwaƙwaf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken da ƙwararrun likitoci suka gudanar ya gano ɓurɓushin sinadarin Diphenhydramine da ake amfani da shi cikin magungunan ciwon ciki, tari, firgici da sauransu.

Sai dai likitoci sun ce adadin da suka gano bai kai ya jawo mutuwar mawakin ba, amma an yi zargin ko jikinsa bai karbi wasu kwayoyi da ya sha ya na raye ba, kuma hakan na iya zama ajalinsa.

An kuma gano wani ciwo a hannun marigayin, duk da dai wannan ma bai isa ya kai ga ya rasa ransa ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Femi Otedola vs Jim Ovia: Manyan attajirai 2 a Najeriya na rigima kan almundahanar kudi

A ƙarshe, likitocin sun haƙiƙance cewa ba za a iya ga abu ɗaya tilo da ya yi ajalin marigayin ba, amma sun ce akwai yiwuwar kwayar da ya sha ba ta gauraya da jinisa ba.

Mutuwar Mohbad: 'Yan sanda suna zargin Primeboy

A baya mun kawo muku labarin cewa ana zargin Ibrahim Owudunni da aka fi sani da Primeboy da hannu dumu-dumu cikin mutuwar Mohbad.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa ya ce Mohbad da Primeboy wanda aminan juna ne sun yi faɗa a bikin mawaƙa a Ikorodu, a nan ne ya ji ciwon ajalinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel