Latest
Da safiyar Laraba bayan fara zaman kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a Edo, an jiyo karar harbe-harben bindiga, lamarin da ya tada hankulan lauyoyi da alkalai.
Jam'iyyar PDP ta shiga jimami bayan rasuwar dan takararta na kansila a jihar Osun. Dan takarar na kansila ya rasu bayan ya yi fama da wata 'yar gajeruwar jinya.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya dakatar da mai taimaka masa ta musamman kan zarge-zargen da ake mata na damfarar mutane kuɗaɗe masu nauyi.
Ƴan bindiga sun kai hari asibitin Kankara da ke jihar Katsina inda suka harbi wani likita tare da yin garkuwa da wasu mutane 5. Jami'an tsaro sun bi bayan miyagun.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kogi. Hatsarin wanda ya auku bayan wata babbar mota ta kwace ya jawo asarar rayukan mutane shida.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai cigaba da ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya. Shugaban kasar ya bukaci hadin kan 'yan kasa.
Kungiyar mazauna jihar Kaduna a karkashin kungiyar BEPU ta shawarci gwamnatin tarayya da ta rungumi tsarin da Gwamna Uba Sani ya dauka a kan 'yan ta'adda.
Goyon bayan Isah Liman Kantigi ga Gwamna Bago a 2027 ya jawo cece-kuce. Jam'iyyar PDP ta sha alwashin daukar matakan ladabartar da dan takarar na ta.
Gwamma Muhammed Umar Bago ya shawarci gwamnonin Arewa su maida Hausa ya zama yaren da za a rika koyar da ɗalibai a makarantun firamare da sakandire.
Masu zafi
Samu kari