Ana Jimamin Rasuwar Daso, an Sanar da Mutuwar Wata Matashiyar Jarumar Fina-Finai

Ana Jimamin Rasuwar Daso, an Sanar da Mutuwar Wata Matashiyar Jarumar Fina-Finai

  • Yayin da ake cikin jimamin mutuwar Saratu Gidado a Kannywood, wata jarumar Nollywood ta riga mu gidan gaskiya
  • Marigayiya Adejumoke Aderounmu kamar yadda aka sanar ta yi bankwana da duniya ta na da shekaru 40 a duniya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan uwan marigayiyar, Adeola Aderounmu ya fitar inda ya bayyana shirye-shiryen binne ta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – An sake shiga jimami bayan sanar da rasuwar jarumar fina-finan Nollywood, Adejumoke Aderounmu da shekaru 40.

Aderounmu ta yi kaurin suna a shirin fim mai dogon zango na ‘Jenifa’s Diary’ wanda ta fito a shirin a matsayin Esther.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya saɓawa Sarkin musulmi, ya yi sallar idin karamar Sallah a Sokoto

Jarumar fina-finai ta riga mu gidan gaskiya da shekaru 40 ana jimamin rasuwar Daso
Bayan rasuwar Daso, wata jarumar fina-finan Nollywood ta rasu. Hoto: Adejumoke Aderounmu.
Asali: Facebook

Yaushe aka sanar da mutuwar jarumar?

Dan uwan marigayiyar, Adeola Aderounmu shi ya tabbatar da mutuwar tata a jiya Litinin 8 ga watan Afrilu, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeola ya kuma bayyana yadda za a gudanar da tsare-tsaren bikin binne ta a cikin sanarwar da ya yi inda ya yi mata addu’ar samun rahama.

Aderounmu ta fara shirin fim dinta na farko a shekarar 2008 a wani fim mai suna Arugba wanda Tunde Kelani ya shirya.

An bayyana inda za a binne jarumar

Kamar yadda aka sanar za a yi bikin binne ta a cocin Baptist da ke garin Owu a yankin Totoro da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

An haifi marigayiyar a ranar 26 ga wata Maris na shekarar 1984 wanda a yanzu ta cika shekaru 40 kenan a duniya.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana ainihin silar mutuwar jarumar ba, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: ’Yan sanda sun bankado shirin kungiyoyin addini da siyasa domin rikita Kano

Fitacciyar jarumar Kannywood, Daso ta rasu

A baya, mun kawo muku labarin cewa Allah ya karbi rayuwar fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Saratu Gidado.

Marigayiyar da aka fi sani da Daso a cikin fina-finai ta rasu ne da safiyar yau Talata 9 ga watan Afrilu a birnin Kano.

Wasu majiyoyi daga iyalanta sun tabbatar cewa Daso ta rasu ne bayan kammala sahur inda tuni aka gudanar da sallar jana'izarta a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel