Fitacciyar Jarumar Fim, Fatima Sa'id Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Fitacciyar Jarumar Fim, Fatima Sa'id Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa daya daga cikin fitattun matan masana'artar shirya fina-finan Hausa, Fatima Sa'id rasuwa
  • Jarumar wacce ke fitowa a matsayin Bintu a shirin Dadinkowa na Arewa 24, ta rasu ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu
  • Kamar yadda shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Abba El-Mustapha ya bayyana, jarumar ta rasu ne bayan ta yi fama da rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa, Fatima Sa'id wacce ke fitowa a matsayin Bintu a shirin Dadinkowa ta riga mu gidan gaskiya.

Jarumar ta rasu ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu sakamakon rashin lafiyar da ta yi fama da ita.

Jarumar fim Fatima Sa'id ta kwanta dama
Fitacciyar Jarumar Fim, Fatima Sa'id Ta Riga Mu Gidan Gaskiyan: Hoto: Youtube/Arewa24, abbaelmustapha1/Instagram
Asali: UGC

Shugaban hukumar tace fina-finan Hausa na jihar Kano, Abba El-Mustapha shine ya sanar da labarin mutuwar jarumar a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Bidiyon ‘dan majalisar Kano yana rutsa Gwamnan CBN kan maida ofisoshi zuwa Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a shafin nasa:

“INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN BINTU DADINKOWA TA RASU
“Allah yayi wa Jarumar da take fitowa a matsayin Bintu ta shirin Dadinkowa na tashar Arewa 24 ta rasu yau Lahadi sakamakon rashin lafiya da ta sha fama da shi.
“Allah Ya gafarta mata yasa Aljanna ce makomarta. Idan tamu tazo Allah yasa mu çıka da kyau da İmanı.”

Jama'a sun yi alhinin rashin Bintu ta Dadinkowa

sulgaz_collections ta yi addu'a:

"Allaah ya ji k'anta da rahama.

official_manlike_priceless:

"Allah ya jikan ta."

farovq_balancy:

"Allah gafarta mata"

amy_koki:

"Allah ya jiqanta da rahama ya Gafarta mata ameen ya Rabbal Alameen"

aysha_buba1:

"Innnlillahi wa inna ilaihi rajiu'n "

nusaybatu_____:

"Allah ya kyautata makwanci amin."

awadas_fabrics_ndmore:

"Allahu Akbar Allah yamata rahma."

hauwa.adamu:

"Allahu Akbar Allah yayi mata Rahama Allah yasa Aljanna firdausi makomanta."

habeebay__:

"ALLAH YA JIKAN TA YA YAFE MATA YA SA MU YI CIKA WA MAI KYAU ALLAHUMMA AMEEN ♥️♥️"

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe, matarsa da 'dansa sunyi hatsari a jirgi mai saukan ungulu

An gano jarumar da ta fi kyau a Kannywood

A wani labarin, mun ji cewa hotunan jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ya dauka hankali a soshiyal midiya.

Nafisa na cikin 'yan matan masana'antar da suka tashe a shekarun baya kafin aka daina ganinta sosai a cikin fina-finai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel