Innalillahi Wa'inna Illahi Raji'un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa

Innalillahi Wa'inna Illahi Raji'un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa

  • Fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Hannatu Umar ta kwanta dama
  • Hannatu ta rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta, kuma tuni aka sada ta da gidanta na gaskiya
  • Shugaban kungiyar tace fina-finai na jihar Kannywood, Abba Al-Mustapha ya mika ta'aziyyarsa kan rasuwar abokiyar sana'ar tasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Labari da ke zuwa mana a yanzu shine cewa Allah ya yi wa shahararriyar jarumar nan ta masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Hannatu Umar rasuwa.

Shugaban kungiyar tace fina-finai na jihar Kannywood kuma babban jarumi, Abba Al-Mustapha ne ya sanar da labarin mutuwar jarumar a shafinsa na Instagram.

Allah ya yi wa jaruma Hannatu Umar rasuwa
Innalillahi Wa'inna Illahi Raji'un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa Hoto: abbaelmustapha1
Asali: Instagram

Jarumar wacce ta yi suna a fim dinta na 'Jarumai' ta rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta, kuma tuni aka yi jana'izarta daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Bayyana Matsayinta Kan Shekaru Uku Da Shugaban Sojin Nijar Ya Ce Za Su Yi a Mulki

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJIUN
"Allah yayi wa Jaruma HANNATU UMAR(JARUMAI) rasuwa kuma tuni anyi jana’izarta Kamar yadda Addinin musulunci ya tanadar.
"Muna Addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata kurakuranta yasa Aljanna ce makomarta. Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani.
"R.I.J.F "

Jama’a sun nuna alhini a kan rasuwar Jaruma Hannatu

official_kabir_kn ya yi martani:

“ALLAH sarki ALLAH ya gafarta mata”

falmata_fancy ta ce:

"Allah yataimata rahama natunata a jarumai Allah sarki

legenddanalaji ya yi martani:

"Ya ubangiji yajikan ta yasa tahuta don alfarman Annabi Muhammad S❤️A❤️W❤️

ophicialdanhajiya_ ya ce:

“Allah yamata rahama”

aminu_mirror ya yi martani:

“ALLAH ya jikan ta.”

eeshat_official ta ce:

“Allah yasa ta huta Ubangiji ya kyautata namu karshen.”

real_abbati247 ya ce:

"Allah ya jikan ki da Rahma ."

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

abba_a_dorayi ya ce:

"Allahumma Ameen ya rabbi Allah Ina."

amy_koki ya ce:

"Allahu Akbar Allah ya jiqanta da rahama ameen ya Rabb."

Matashi ya tashi daga Bauchi zuwa Kano don ganin Aisha Humaira

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi mai suna Adamu ya yi tattaki daga jihar Bauchi zuwa jihar Kano domin ya yi ido hudu da shaharriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Aisha Humaira.

Sai dai kuma, matashin ya hadu da sharrin barayi inda suka karbe masa komai a nan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng