Sadiya Haruna Ta Maka G-Fresh Al'ameen a Gaban Kotu

Sadiya Haruna Ta Maka G-Fresh Al'ameen a Gaban Kotu

  • Rigimar da ke tsakanin Sadiya Haruna da mijinta Abubakar Ibrahim (G-Fresh) ta kai su ga zuwa gaban kotu
  • Tsohuwar jarumar ta Kannywood ta maka G-Fresh a gaban kotu tana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu
  • G-Fresh ya tubure yana son matarsa inda alƙalin kotun ya ƙara musu lokaci domin su je su sasanta tsakaninsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Shahararriyar tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna, ta maka mijinta, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke Kano tana neman a raba igiyar auren da ke tsakaninsu.

Jarumar, wacce aka fi sani a TikTok da Sayyada Sadiya Haruna, ta ce ta fahimci cewa mijin nata ba irin wanda take so ba ne, kuma ba za ta iya ƙarasa sauran rayuwarta tare da shi ba, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Sadiya Haruna ta kai G-Fresh kara kotu
Sadiya Haruna da G-Fresh Al'ameen a wajen bikinsu Hoto: @gfresh_alameen
Asali: Instagram

Idan ba a manta ba dai, auren da aka yi tsakanin jaruman na TikTok biyu ya ja hankalin jama'a saboda yadda aka yi ta cece-kuce a kansa.

Yayin da G-Fresh ke zarginta da yin aboki namiji (Besty) wanda ba za ta iya rayuwa ba sai da shi, Sadiya ta ce maganar auren da ke tsakaninsu ta zo ƙarshe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wacce buƙata Sadiya take da ita?

A yayin zaman kotun, Sayyada Sadiya Haruna ta hannun lauyanta Barr. A.B Saka ta buƙaci a raba aurenta da G-Fresh.

Lauyan ya shaida wa kotun cewa a zaman farko kotun ta bayar da izini ga wanda ake ƙara ya nemi afuwar ta amma bai yi ba.

A nasa ɓangaren lauyan G-Fresh, Salihu Umar Kududuffawa, ya shaida wa kotun cewa sun daɗe suna neman ta domin su daidaita auren amma ba a same ta ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Ya buƙaci kotun da ta ƙara musu lokaci domin sasanta ma’auratan saboda har yanzu wanda yake karewa yana son matarsa.

Alƙalin kotun mai shari'a Abdullahi Halliru, ya ba ma'aauratan ƙarin lokaci domin sasantawa sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga Oktoba, 2023.

Radeeya Ta Bayyana Jarumin Da Take Son Aure

A wani labarin kuma, fitacciyar jarumar Kannywood Radeeya Jibril ta bayyana jarumin da za ta iya aura a masana'antar Kanyywood.

Jarumar ta bayyana cewa idan aka ce ta zaɓi wanda za ta aura daga masana'antar, to tabbas ba za ta tsallake jarumi Ali Nuhu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel