Jaruma Radeeya Jibril Ta Bayyana Jarumin Da Za Ta Iya Aura a Kannywood

Jaruma Radeeya Jibril Ta Bayyana Jarumin Da Za Ta Iya Aura a Kannywood

  • Fitacciyar jarumar masana'antar finafinai ta Kannywood, Radeeya Jibril ta bayyana jarumi ɗaya da za ta iya aura daga cikin jaruman masana'antar
  • Jaruma Radeeya ta bayyana cewa jarumi Ali Nuhu ne kaɗai za ta iya aura daga cikin jaruman da ke masana'antar ta Kannywood
  • Radeeya ta bayyana cewa za ta iya auren jarumin ne saboda yadda yake matƴƙar nuna kulawarsa ga matarsa

Jaruma Radeeya Jibril ta bayyana mutum ɗaya wanda za ta iya aura daga cikin jaruman da ke masana'antar finafinai ta Kannywood.

Jarumar ta bayyana cewa jarumi Ali Nuhu kaɗai za ta iya aura a kaf cikin jaruman da ke masana'antar finafinan ta Kannywood.

Jaruma Radeeya ta ce za ta iya auren Ali Nuhu
Jaruma Radeeya Isma'il ta bayyana cewa Ali Nuhu kadai za ta iya aura a Kannywood Hoto: @Realalinuhu, @radeeya_jibril
Asali: Instagram

Jaruma Radeeya ta bayyana cewa akwai ƙauna a tsakaninta da jarumi TY Sha'aban ta ƴan'uwanta ka.

Jarumar ta bayyana hakan ne dai a yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a shirin Nishadi@360 na gidan rediyon Kanawa Radio, wacce Salisu S. Fulani ya sanya a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Yadda Mahaifiya Ta Yi Ta Maza Ta Cafke Dan Ta'addan Da Ya Yi Garkuwa Tare Da Halaka Yarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin shirin an yi wa jarumar tambayar cewa ko a cikin jaruman Kannywood wanene za ta iya aura idan aka ce dole sai ta zaɓo miji daga cikin jaruman masana'antar.

Radeeya ta kada baki ta ce:

"A gaskiya Ali Nuhu zan aura, saboda yadda yake kula da matarsa. Yanayin yadda yake kula da matarsa yana burgeni. Domin tun da ya yi aure ba a taɓa jin wani saɓani ya shiga a tsakaninsu ba."
"Domin idan za ka yi aure idan wanda zaka aura yana da mata za ka tsaya ka duba ka ga ya yake kula da matarsa."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

@turbans_by_hafcy ta rubuta:

"Gaskiya kam tana ruwa Phone Store, kwalelenki yasin bawan Allah yana zaman shi lafiya."

@teegraphics__designs ya rubuta:

To idan aurenku alheri ne Allah ya tabbatar da hakan."

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

@Anty_b_kayan_mata ta rubuta:

"A ƙyale dai Maimuna ta zauna lafiya a ɗakinta dan Allah."

Legit Hausa ta tuntuɓi jarumar domin jin ta bakinta kan waɗannan kalamai da ta yi na son auren Ali Nuhu idan dama ta samu, amma ba ta dawo da saƙon da aka tura mata ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Kin Kara Aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa jarumi Ali Nuhu ya bayyana dalilin da ya sanya ya ƙi yi wa matasara kishiya.

Jarumin ya bayyana cewa yana zaman lafiya da matarsa wanda hakan ya sanya tunanin ƙara aure bai taɓa gitto masa ba, duk ya kai shekara 20 da yin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel