Dalilin Da Yasa Ake Ci Gaba da Ganina a Fim Bayan Na Yi Aure – Jaruma Rahma MK

Dalilin Da Yasa Ake Ci Gaba da Ganina a Fim Bayan Na Yi Aure – Jaruma Rahma MK

  • Jarumar masana'antar Kannywood, Aishatu Auwalu ta tabbatar da cewar tana ci gaba da fitowa a fina-finai ko bayan aurenta
  • Aisha, wacce aka fi sani da Rahma MK ta ce ta samu cikakken goyon baya daga wajen mijinta a lokacin da ta nuna masa aniyarta na son ci gaba da sana'arta tun kafin aurensu
  • Sai dai kuma, ta ce ya bata shawarar ci gaba da kame kanta kamar yadda ta saba yi kafin ta zama matar aure

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Aishatu Auwalu wacce aka fi sani da Rahma MK ta magantu kan dalilinta na ci gaba da fim duk da ta yi aure.

A shekaru biyu da suka gabata ne jarumar wacce ta shahara a cikin fim mai dogon zango na ‘KwanaCasa’in’ ta shiga daga ciki.

Kara karanta wannan

"Na siya bokitin shinkafa 1 kan N3,000": Matashiya ta gano kauyen da ake siyar da shinkafa mai sauki

Rahma MK ta magantu kan aure da fim
Dalilin Da Yasa Ake Ci Gaba da Ganina a Fim Bayan Na Yi Aure – Jaruma Rahma MK Hoto: rahamamk
Asali: Instagram

Sai dai kuma ko bayan aurenta ta ci gaba da fitowa a fina-finai kamar dai yadda ta saba a baya lamarin da ya dungi ba mutane mamaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharadi 1 da mijina ya gindaya mani kan fim, Jaruma Rahma

A wata hira da jaridar Daily Trust ta yi da ita, jarumar ta tabbatar da cewar ta nunawa mijinta ra'ayinta na son ci gaba da harkar fim kafin ta aure shi wanda shi kuma ya amince.

Sai dai kuma, ta ce babu wani sharadi da ta gindaya masa kan haka kafin auren nasu, illa dai ya bukaci da ta ci gaba da kame kanta a yayin fim kamar yadda ta saba tun kafin aurensu.

Ta ce:

"Namiji shine mai iko kan mace a lamarin aure. Ban gindaya mai wani sharadi ba. Na kuma gaya masa cewa ina son ci gaba da sana’ata, ya amince.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

"Sharadi daya tilo da ya gindaya mani shine in ci gaba da kame kaina a lokacin aikina, kamar yadda nake yi kafin aure. Kuma ina ganin wannan ya fi kama da shawara ba sharadi ba.

Yadda nake kula da mijinta da fim, Rahma MK

Kan yadda take hada fim da kula da miji, jarumar ta ce ta kan sanar da shi tun kafin lokaci a duk san da za ta fita.

Ta kuma ce sai ta gama kula da lamuransa gaba daya tukuna, sannan idan ya fita ita ma sai ta shirya ta fita wajen daukar fim.

Jarumar ta kuma bayyana cewa bata dadewa a wajen daurkar shirin fim, kuma ta kan koma gida da wuri saboda ita din matar aure ce.

Adam Zango ya magantu kan aurensa

A wani labarin, mun ji cewa shahararren jarumin Kannywood, Adam A Zango, ya ce ya kamu da lalurar tsananin damuwa bayan mutuwar aurensa.

Zango ya ce lamarin ya kai har sai da ya ja baya a wasu harkokinsa a lokacin da aurensa da tsohuwar matarsa, Safiyya Umar Chalawa, ya mutu a watan Afrilun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel